ZUWAGA MA’AURATA MATA YA KAMATA KU RIKE WANAN

ZUWAGA MA’AURATA MATA YA KAMATA KU RIKE WANAN

Abubuwan da ya kamata
Ki bari yai miki ko kice
Yai miki.

Kunshi
Ki koya masa yanda ake sa lallai a hannu don wataran yasa miki
Idan kina son nail polish sanda duk kike menses sai ki bashi ya shafa miki.

Bashi dankunne ya sa miki. Ko agogo ko awarwaro ko ma sarka.

Juya ya zuge miki zif
Sama ko kasa.

Inkin wanki kanki, ya bushe. Hada hair oil ki bashi yai miki oiling gashin

Bashi mai ya shafa miki a baya. Musamman idan man mai kamshi ne.

Ki bari yaga yanda kike kwalliya. Musamman a ina kike sa turare a jikinki.
A wuya, a kasan guiwarki, a hammata,abayan kunne da cibiya. Shafe duk jikinki.
Ki bari ya gani.: Abubuwan da ya kamata
Kuyi tare.

At least sau daya kuyi sallah tare.

Kuci abinci tare

Ku yiwa juna karatu ko da wani bangare ne a jarida ko dan labari.

Cuddle up don yana kara shakuwa.

Share your ear piece.
Wani dan peace of wa’azi kika samo ko joke ko ma wata love song.
Sa masa kunne daya, kisa kunne daya kuji tare.

Help him shave. Amma don Allah karki yanke shi.
Be very gentle. Show tenderness and love.

Yanke masa farce ki bashi foot bath.
Musamman idan a gajiye yake.

And jefi jefi don karawa kauna da armashi
Have a pillow fight
Kuyi wasan lido ko snake and ladders.
Duk abinda zai jawo raha da farin ciki a rayuwarku to kuyi.

Ita rayuwa guda daya ce.
In lokaci ya wuce baya dawowa.
Kuma abinda kuka yi shi kuke tunawa.
So me zai hana ku gina abinda in kun tuna zakuji dadi?
A ko da yaushe su muke mu shiga ran mazajen mu ba mu bari suyi kyamar mu har ju janye jiki ba.
So muke suyi ta doki da alfahari .
Abubuwan da ko kusa karki yarda kiyi su a gaban miji.

Tsifar kai Musamman idan kitson ki yai tsufa.

Daurin kirji, sai dai in wanka kika shiga.
Ko wankan ma, make it stylish & sexy. How?
Ki kama bakin zanin duka biyu, ki daura a kijiki ki kulle, yanda zai zauna das a kirjinki yayi kuma lebatu wic looks very sexy.

Karki yarda ki tauna kashi a gaban miji.
Domin taunar kashi da shan rake kan canza yanayin mutum.
In har kina so kici kashin bari sai bakwa tare.

Idan ke maici ce sosai, karki bari miji ya ganki da tulin abinci a gabanki.
Yi kokari kici rabi kafin ya dawo don kinga in zaki kara kadan zaki diba.

Don Allah karki gyatsa ko tusa a gaban miji.
I beg you.

Karki sakace ko kaki pls.

Karki kuskura kiyi soshe soshe domin Bera ce kawai take wannan halin.
Allah kiyashe mu.

Karki yi karya a gaban sa.

Karki zagi, karki kuskura ko da kuwa an bata miki.
Musamman Ashar.
Karki ki yarda.

Kar ki kawo masa gulma domin zaki zubar da kimar ki a idonsa.

Karki yarda ya ganki da kaushi don Allah…

Allah yasa mu dace da fatan zamu gyara rayuwar aure ba abin wasa bane

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *