Zaman lafiyar ki da miji shi ne ki kiyaye wadannan abubuwa dan a wajen namiji reni ne, kuma sukan iya haifar da tsanar ki a zuciyar sa.
Musu dashi
Ya fada ki qi yi
Ya sa doka ki tsallake
Ya fada kina fada
Daga murya fiye da nashi
Ya miki abu ki rena
Ya buqaceki a shimfida ki nuna kamar alfarma kike masa da kike bashi kan ki
Ki yaba wasu fiye dashi
Ya baki abu ki karba ko ki ajiye a wulaqance
Ya miki abu ba godiya
rashin tausaya masa
Maimaita abun da kin san yana sosa masa rai
Ki nuna tilasci yi miki abunda bai zama tilas ba
Qasqantar dashi a idon wasu
Nisantar kiran sa a shimfida
Yi masa gadara da iko akan wani abu
Wulaqanta mahaifiyar sa
Nuna masa wani yana abunda bayayi a gidan sa
Sa shi yana abunda yafi qarfin sa a gidan sa dan fitinar ki.
Zagin sa
Wulakanta shi, iyanyen sa ko ‘yan uwan sa
son tilasta masa yin abun da baya so
Sa ido akan rayuwar aikin sa da mu’amalar sa da mutanen sa
Sa masa sharadi akan abunda baki da iko a kai ko sai ya miki abu kafun ki amince masa da buqatar sa
Zaba masa wadda zai mu’amalanta
Kyaman ‘yan uwan sa
Kai shi qara wajen mutane
Masa bincike, kwakwafi da babakere a rayuwar sa
Shigan masa cikin ‘yancin sa na fita, spending kudin sa, mu’amala da dangi, abokanai ko abokanan hulda.
Shisshigi da babakere tsakanin sa da dangin sa da abunda yake musu.