Kamar yanda kuka sani, olsa kurji ne da ke samun tumbi ko hanjin dan adam.
Abubuwan da ke kawo olsa ko kuma suke iya tada OLSA su ne
shan maganin kashe ciwo ba akan ka’ida ba
yawan cin abu mai yaji ko twanka
yawan cin maiko
yawan shan abu mai zafi
yawan shan Lipton ko nescafe musamman wanda ba a saka madara ba.
rashin cin abinci a cikin lokaci
damuwa da yawan tunani.
MATAKAN DA YA KAMATA MAI OLSA YA DAUKA KAFIN WATAN AZUMI
Ya kamata mai OLSA ya fara daukan matakai tun kafin shigowan watan Ramadan.
Daga cikin matakan da za’a iya dauka sun hada da
shan maganin OLSA a kan ka’ida
shan magani sama da daya. Ma’ana Kada mutum ya sha magani kwara daya tilo domin OLSA na buÆ™atar magunguna biyu ko ukku
shan maganin OLSA iya lokacin da a ka kayyade. Akwai maganin da ya kamata a sha har tsawon sati biyu, akwai na kwana goma. Duka ya kamata a shanye su.
rage cin abin da ke iya tada olsa. Alal misali abu mai zafi, abu mai yaji, abu mai maiko dayawa.
MATAKAN DA YA KAMATA A DAUKA A CIKIN WATAN RAMADAN
Yin sahur
jinkirta sahur kamar yanda addini ya karantar
kada a kwanta bayan cin abincin sahur, domin yin haka na iya tada OLSA
shan maganin olsa bayan cin abincin sahur
kada a ci abu mai yaji ko maiko ko lipton ko nescafe mara madara a lokacin sahur
yin bude baki a cikin lokaci
shan abu mai dan sanyi a lokacin bude baki
cin dabino a lokacin bude baki
shan maganin OLSA bayan bude baki
kada a cika ciki sosai a zama daya bayan yin bude baki. A na son a ci abinci kadan kadan bayan mintuttuka ko awa
shan kayan gona irin su ayaba. Kada a yi saurin shan laimu.
Idan an dauki wadannan matakan in shaa Allah za a samu sauƙin yin azumi musamman ga mai OLSA.
Akwai wadanda OLSA din su ya nada tsanani sosai ta yanda basa iya azumi. Ire-iren waÉ—annan mutane ya kamata su ga ma’aikatan lafiya.
Allah Ya sa mu dace.