Abubuwan hadawa
- Fulawa
- Nikakken nama
- Kabeji
- Karas
- Albasa
- Kwai
- Magi
- Gishiri
- Curry
- Brush
- Mangyada
Yadda ake hadawa
Da farko zaki wanke kabejinki kiyanka da albasa d karas sannan kisoyasu da mai cokali daya kuma suyan ya zama na sama-sama sannan sai ki zuba nikakkaen namanki da magi da gishiri da curry.
Jim kadan saiki sauke daga kan wuta bayan nan sai ki hada fulawa kwai magi gishiri da ruwa saiki kwaba yayi kamar kaurin wainar fulawa sai kuma ki shafa mai a nonstick sannan sai ki shafa fulawarki da burosh.
Idan yayi zakiga gefen ya dago sai ki cire ki tara su idan kin gama saiki dinga dauka kina zuba hadin kabejinki kina nadewa kamar tabarma haka zaki rinkayi idan kingama sai ki saka manki awuta sai ki rinka soyawa harkigama
Allah yakarbi ibadunmu