YANDA AKE YIN GULLISUWA MAI DADI

Abubuwan da ake bukata :

  • Madara 4cups
  • Sugar 2cups
  • Flavor
  • Condensed milk ( optional).
  • Ruwa
  • Yanda ake hadawa:

Da farko za’a samu plastic rubber ko bowl, sai a zuba madara adan bude ta atsakiya sannan a kawo sugar shima a zuba a yamutse su hade , sai azuba flavor ( optional) in anaso shima za’a zuba ahada su tare. Bayan nan sai a kawo ruwa ( ana samun matsala a wurin zuba ruwa da an cikasu don madara bata raina ruwa sai an lura ) sannan ana zuba condensed milk a wurin kwabin but it’s optional ( Amma in kina so yayi tauri to sai ki zuba ta) sai a kwaba kar a bari yayi ruwa kuma kar yayi karfi sosai, sai a samu tray ko plate ana diba ana mulmulawa yanda ake so ana ajewa . Bayan nan sai a aza man gyada bisa wuta idan yayi zafi said a dinga dauka ana soyawa bayan yayi sai a barshi yahuce.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *