YANDA AKE MAGANCE FASO KO KAUSHIN KAFA (CRACKED HEELS)

Faso ko kaushi nafaruwane yayin da fatar tafin kafa ta bushe kuma tayi karfi sannan matsa tafin kafar yayin tafiya yasanyashi ya tsage. Abubuwan dakan janyoshi sun hada da kiba mai yawa, sanya budaddun takalma kamar sandals, lokacin sanyi da kuma in mutum yanada busheshshen fata.
Ana samunshi a jikin manya harda yara. Kuma anfi samunshi a jikin mata fiye da maza.

Hanyoyi maganceshi sune :

 1. Amfani da man tafin kafa (heel balms) ko mayuka masu kauri (thick moisturizers) : Amfani da ire iren mayukan nan sune farkon abinda mutum yakamata yafara amfani dashi. Yin amfani da mayuka masu Urea (Flexitol heel balm), salicylic acid (Kerasal), alpha-hydroxy acid (Amlactin) da saccharide isomerate suna matukar taimakawa wajen sanya taushe da fidda mataccen fata. Kyau mutum yashafa da safe.

Wasu daga cin mayukan kan kawo irritation da stinginess awajen, wanda ba wani matsala bane, idan man natakurama mutum sosai yakamata yagarzaya wajen likita.

 1. Tsuma kafafuwa cikin ruwan sabulu na minti 20, sannan agoge kafan da dutsen kafa ko foot scrubber. Sai awanke da ruwa sannan ashafa moisturizer ko heel balm, sai a shafa petroleum jelly (Vaseline), sai a saka safa.
 2. Amfani da liquid bandage
 3. Amfani da Zuma : Shafa bayan an dirje kafa ko kwanciya dashi da daddare na taimkawa wajen warkar, wankewa da moisturizing fata.
 4. Amfani da man kwakwa

Wasu hanyoyin sun hada da

 • Amfani da vinegar (khal) wajen tsuma kafa
 • Amfani da man zaitun
 • Amfani da man kade/kadanya
 • Amfani da dakakken ayaba
 • Amfani da paraffin wax
 • Amfani da oatmeal da mai

Abin kula kuma shine adaina amfani da hannu ko razor wajen cire fatan daya dago yin haka nakara bata kafa kuma kada agoge kafa yayin dayake abushe.

Please share! Don wasu su karu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *