Abubuwan da zaki nema
- Mangoro manya masu tsoka
- Danyar citta
- Apple cider vinegar (khal tuffa)
Yanda zaki hada
Da farko za a samu ruwa cikin mazubi mai tsafta da fadi a zuba ruwan khal tuffa murfi 2 acikin ruwan sai a zuba fruits din acikin ruwan a wanke tas a kuma zuba su acikin wani ruwa daban a wanke a ajiye gefe daya.
Sai a yanka wannan mangoron a cire dik tsoka da take jikinsa a zuba a blender a fere cittar a wanke a zuba a cikin blender, a zuba sugar da ruwa a markade suyi laushi sosai a juye a mazubi daban a saka ice block (kankara) a juya, shikenan an kammala sai Sha.