GYARAN JIKI.
Ina son na ruga da gudu don yi
maku bayani kan amfanin ganyen
Magarya, musamman ga mace.
Ganyen yana dauke karni da warin
jinin haila, biki da sauransu. Duk
kuwa da cewa mun taba yin
magana a kan wannan ganyen
amma har yanzu masu
karatu na neman karin bayani.
Abin sani shi ne Magarya na da
taimako ainun ga dan adam,
musamman mace. Yana taimakawa
wajen warkar da mugunyar warin
gaba ga mata.
Har ila yau, Magarya tana warkar
da kwayoyin cututtuka masu tarin
yawa a jiki. An fi son a yi amfani
da danyen sai dai in hakan bai
samu ba, za a iya amfani da
busasshe. Yadda ake sarrafa shi
kuwa shi ne a murza ko kuma a
daka shi, inda hali a gyara shi,
sannan a nika shi za a ga ya yi
kumfa kamar kumfar sabulu.
A lura, yayin da uwargida ke
amfani da ganyen wajen wanke
jiki, za ta ga yana dan yauki, haka
kuma duk wani dadadden datti, zai
rika fita. Bincike ya nuna cewa
babu sabulun da ya kai ganyen
Magarya fitar da datti a jikin dan
adam.
Karin Bayani Game Karin
Ni’imar Mace
Kamar yadda muka sha yin bayani
a baya dangane da karin ni’ima a
jikin mace, har kullum muna dada
fadada wannan bangaren, inda a
kullum masana harkar kiwon lafiya
ke gudanar da karin haske kan
wannan batu.
Uwargida za ki iya samun
sassaken Baure, ki dafa shi sai
bayan ya dafu sai ki juye ruwan
sai ki samu mazarkwaila da zuma
da kanunfari da citta, ki zuba aciki,
ki tafasa ki rika sha safe da
yamma.
Masana tun tabbatar da cewa
dukkanin macen da ke amfani da
wannan, za ta samu karin ni’ima a
jikinta, sannan ta kasance mai
dimbin alheri ga maigidanta.
Bayan haka, za ki iya samun
totuwar rake mai tsafta, sai ki bar
shi ya bushe, ki samu Bagaruwa
guda uku da Almuski da
Kanumfari, ki hada su, waje daya
ki rika tsuguno kuma ki rika goga
zaitun a jiki, musamman a
gabanki, hakan zai kara miki
ni’ima mai yawae.
Bayan wannan, za ki iya samun
RIDI, ki wanke shi, ki nika har sai
ya zama gari, ki b