Yan Nigeria Nayi Alkawarin Zan Dora Daga Inda Shugaba Buhari Ya Tsaya Cewar Bola Tinubu

Asuwaju Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa” idan yayi nasarar samun mulki a 2023 Zai Ɗora Daga Inda Buhari Ya Tsaya Har Sai Inda Ƙarfi sa ya kare, Cewar Tinubu.

Daga Shafin gidan jaridar vanguard na Nigeria a wata shira da muka samu daga bakin manema labarai cewa” dan takarar shugabancin kasar Nigeria Tinubu ya bayyana cewa.

Matukar yayi nasarar samun zaben 2023 to zai dora daga inda buhari ya tsaya akan gudanar da mulkin Nigeria a cewar dan takarar Asuwaju Bola Ahmad Tinubu na Jam’iyyar (APC) a Nigeria.

Bola Ahmad tinubu ya bayyana hakan ne yayin wani taro daya gudana a babban birnin tarayyar na nigeria dake abuja kan cewa idan yayi nasarar samun shugabancin nigeria to zai dora daga inda Buhari ya tsaya insha Allah.

Yayin da wasu daga cikin ‘yan nigeria suke bayyana ra’ayin su, dangane da wannan batu kan cewa” basu yarda da wannan maganar ba domin kuwa ansha su, sun warke.

Babu wani mutum da zai Kara zuwa musu da dadin baki matukar yasan bazai iya cika musu da burin suba na rayuwa hakika mafiya yawan masu mulkin kasar nigeria basu da adalci.

Domin ko wani dan siyasa daga lokacin da yayi nasarar samun mulki to zai kasance daga ‘yan uwansa sai matan sa, sai kuma ya’yan cikin sa zasuyi ta almubozaranci, da dukiyar talakawan, kasar Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *