YADDA ZOBO KE MAGANCHE MATSALOLIN DA SUkA SHAFI MARA

Zobo wani sanannen ganyene da mutane ke tafasawa ko jikawa asha kuma zaa iya kwadashi aci wanda mafi akasari ana nomashi ne a arewachin Nigeria.

Wannan ganye da ake sha yana kunsha da wasu muhimman sunadarai wadanda suke taimakwa sosai wajen bunkasa lafiyar dan adam.

Wadanda suka san amfanin zobo mafi akasari sunfi amfanindashi wajen bunkasa yawan ruwan maniyyi ( sperm count ) ga namiji wanda rashin yawan ruman maniyyi na daya daga cikin abubuwanda kesa rashin haihuwa ga maza.

Bayan haka zobo yana kashe kwayoyin cutar bacteria dake kama farjin mata daku infection din da ke kama mahaifa wanda shima barazanane ga mache mai neman haihuwa.

YADDA AKE AMFANI DA ZOBO DOMIN NEMAN HAIHUWA.

Duk mai neman haihuwa mace ko namiji ko son maganche wasu cututtuka da ake iya dauka wajen saduwa to zaa rika dafa zobo da citta bayan sun dahu atache adan kara ruwa asha kofi daya kafin aci komai kullum da safe.

GARGADI.

Baa sha da sukari

mace mai yaron ciki ko tsohon ciki bata shan zobo domin yana kunshe da wasu sunadarai daka iyasa zubewar cikin kokuma a haifi jaririn kafin ya isa haihuwa.

Allah yasa mudache ameen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *