Zakkar fidda-kai Sadaka ce da Manzon Allah {SAW} ya farlanta ta yayin da aka gama azumi.
An kira ta zakkar fidda kai ne saboda tana wajaba ne idan an gama Azumin Ramadan gabadaya.
Zakkar Fidda-kai wajibi ce akan dukkan musulmi, wanda ya mallaki sa’i daya na abinci kamar kwano daya kenan wanda ya fi yawan abin da zai ciyar da iyalansa.
Mai ba da zakkar zai fitar wa da kansa, matarsa, da duk wanda ciyar da shi take kansa, har ma jaririn da yake cikin ciki.
An fi son a fitar da zakkar fidda kai ranar Idi, bayan alfijir ya 6ullo kafin sallar Idi. Kuma ya halatta a gabatar da ita kafin ranar idi da kwana daya ko biyu, saboda sahabbai sun yi haka.
Ba ya halatta a jinkirta ta har bayan idi.
WADANDA AKE BAWA ZAKKAR FIDDA-KAI
Ana bawa wadannan mutanen guda takwas zakkar fidda kai, saboda sun shiga cikin faxin Allah Madaukakin Sarki “Kadai Sadaka a bawa faqirai …”. (Attauba : 60)
Abu Sa’id Al-khuduriy – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Mun kasance muna fitar da zakkar fidda kai daga abinci a zamanin Manzon Allah (SAW) ranar qaramar sallah”
Abu Sa’id ya ce, “Abincinmu a wannan lokaci kuwa shi ne Sha’ir da zabibi da cukwi [Cukwi : Shi ne nonon da ya bushe, a na girki dashi da dabino (Bukhari).
HIKIMAR ZAKKAR FIDDA-KAI
Tsarkake mai azumi daga maganganun wofi da na batsa, saboda abin da aka rawaito daga Abdullahi dan Abbas – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Zakkar fidda kai tsarki ce ga mai azumi daga maganganun banza da ayyukan batsa, kuma ciyarwa ce ga miskinai”[Abu Dawud ne ya rawaito shi].
Saboda mafi yawanci mai azumi ba ya rabuwa da maganganun da basu da amfani da wasannin shirme, da maganar da ba ta da fa’ida, to wannan sadakar sai ta zamar masa tsarki daga irin waxanncan maganganun haramun da ya yi, waxanda suke rage ladan ayyuka, suna rage azumi
Yalwatawa miskinai da talakawa, da wadatar da su ranar idi daga roqon mutane, roqon da yake dauke da qasqanci da wulaqanci a ranar idi, wadda take rana ce ta farin ciki da murna, sai su yi tarayya da mutane cikin farin cikin ranar idi.