Assalamu Alaikum Warahmatullah wabarakatuhu yan uwa barkan mu da war haka muna muku fatan Alkhairi,da fatan muna cikin koshin lafiya
A yau zanyi bayani ne game da maganin sanyin mara na maza da mata,kuma wannan magani ne sadidan mujarrabun kaifiyyan la shakka fihi insha allahu
ABINDA ZA’A NEMA
- ganyen zogale moringer
- Ganyen raihan basil
- Kanun fari clove
- Citta Ginger
- Tafarnuwa Garlic
Za’a samu abubuwan da muka lissafa amma kowannen su busashshe ake bukata, sai a hade waje guda a dake su ko ma niÆ™e su,suyi laushi.
Za’a rika diban karamin chokali a zuba a shayi ba madara Tea a barshi na tsawon minti 5 sai a sha,zaai haka sau 2 a rana
Idan mace na ciwon mara da debi chokali 2 babba ta tafasa da ruwa kofi 2,idan ya wuce sai tasa zuma,tasha kofi 1 safe 1 yamma
Za’ai amfanin dashi na tsawon sati 2 zuwa wata 1 insha allahu za a samu lafiya