Abubuwan da za’a bukata
Kaza
Dakakken masoro
Nikakken citta
Garin tafarnuwa
Kori
mangyada
Borkono (ga mai bukata)
Kabeji
Timatir
Gurji
Albasa
YADDA AKE SARRAFAWA
Da farko dai za’a wanke kaza a kumacire karninsakamar yaddana yi bayania baya. Bayan haka sai a yayyanka shi sannan a zuba a roba. Sannan a zuba nikakken
masoro da garin citta da garin tafarnuwa da kori da dakakken borkono ga mai bukata sannan a zuba cokula biyu na man zaitun sannan a cakudasu sannan a zuba a leda a sanyasu a firiji na tsawon a wanni biyu zuwa uku. Bayan haka sannana
saiki gasasu agarwashin wuta ko kumana’uraryingashiharsai kaza ta gasu. Sannan a kwashe a ajiye a gefe. Sannan a yayyanko kabeji kanana da albasa da kuma gurji sannan a zuba su a ciki a cakudasu sai a sake yaryada soyayyen man zaitun din kadan akai da magi. Za’a iya cin wannan hadin da jus din lemun zaki mai sanyi. A ci dadi lafiya