YADDA ZAKU GYARAN FUSKA DA RUWAN KWAI DA ANFANINSA

gyaran fuskar mutum kamar haka

Ruwan kwai nada sinadarin gina jiki, da kuma sinadaran Bitamin
Ruwan kwai na rage tsufar fuska Danyen ƙwai
Danyen kwai na kare fuska daga yawaitan fitar kuraje
Danyen kwai na kara ma fuska haske
Ruwan kai na rage kumburin idanu Yadda ake hada ruwan kwai don samun bukata shine, za’a fara turara fuska da ruwan zafi, sa’annan abi da Rose water a shafe fuskar, kamar yadda majiyar mu ta ruwaito

Daga nan sai a fasa kwai, a cire kwaiduwar, sai a kada farin ruwan kwan, har sai yayi kumfa, bayan nan sai a shafe fuska da wannan ruwan kwai, sai kuma a daure fuskar da takardar ‘Tissue’ a manna a fuskar, a kara samun takardar a sake mannawa a dukkanin fuskar.

Da zarar fuskar ta bushe a haka, sai wanke fuskar, sa’annan a shafe fuskar da kwaiduwar ita ma, sa’annan a wanke, idan an cigaba da wannan tsari, za’a samu biyan bukata.

ku cigaba da kasancewa damu a koda yaushe domin samun abubuwa gyra

mungode

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *