YADDA ZAKU AGANCE LAULAYI DA MAGUNGUNAN TAZARAR HAIHUWA SUKE HADDASAWA (TREATMENT FOR SIDE EFFECTS OF FAMILY PLANNING METHODS)

Nayi wannan rubutun ne saboda yawan korafin da ‘yan-uwa mata sukeyi akan laulayin da magungunan tazarar haihuwa suke haifarwa.

Magance laulayin ya danganta ne da irin maganin da mace tayi amfani dashi da kuma nau’in laulayin. Kadan daga cikin laulayin da akafi samu, da kuma hanyoyin magancesu sune:

  1. Magungunan tazarar haihuwa wadanda akeyin amfani da sinadarai (hormonal methods): wannan ya kunshi dukkan magungunan tazarar haihuwa na kwayoyi (pills), allura (injections), na’urorin da ake sanyawa a karkashin fata (patches). Ana kiransu da magungunan tazarar haihuwa na sinadarai ne saboda ana yinsu da sinadaran estrogen da progesterone. Laulayin da suke haddasa sune:

a. Tashin zuciya (nausea). Shansu tare da abinci yakan rage yiwuwar samun tashin zuciya. Ma’ana, a hada tare da abinci a lokacin da za’a sha.

b. Bacin rai (mood swings). Idan mace tana shige cikin yanayin bacin rai sakamakon amfani da magungunan, to, ta koma asibiti domin a duba yiwuwar canza mata da wanda bazai sanyata bacin rai ba, ko kuma a canza mata adadin lokutan da yake sha (dosage change).

c. Rikicewar al’ada (irregular periods). Macen da ta sami wannan matsalar, ya kamata ta koma asibiti domin a duba yiwuwa canza mata maganin zuwa wanda yake da karancin estrogen a cikinsa (low-dose estrogen).

d. Ciwon nono (breast tenderness). Matan da suke shan kwayoyin combination pills masu dauke da estrogen da progesterone kamar Levofem, Yasmin, Alesse, Loestrin, da sauransu. Idan mace ta sami laulayin, to, tayi hakuri domin zai bari da kansa. Idan bai bari ba, ko kuma ta damu, sai ta canza zuwa maganin only pill wanda ya kunshi sinadaran progesterone kadai, kamar norethindrone, Norgeston, Noriday, desogestrel, Cerazette, da sauransu.

  1. Hanyar tazarar haihuwa wacce ake sanya na’urori a cikin mahaifa (intrauterine devices): na’urorin iri biyu ne. Akwai na copper mai suna “Mirena” kuma akwai na sinadari mai suna “Kyleena”. Laulayin da suke haddasa sune:

a. Ciwon mara ko ciki (cramping). Ana yin amfani da magungunan kashe radadi na gama-gari (over the counter pain relievers), kamar ibuprofen, naproxen, diclofenac, aspirin, ketoprofen, acetaminophen, buscopan, paracetamol, da sauransu.

b rikicewar al’ada (irregular periods). Idan na’ura ce ta haifar da rikicewar al’ada, to, akwai bukatar mace tayi hakuri ta jira har na dan lokaci mai tsawo, domin yakan daidai da kansa bayan watanni. Idan bai daidaita ba, to, ta koma asibiti domin a canza mata da wata na’urar.

  1. Hanyar tazarar haihuwa wacce ake amfani da makari (barrier methods): wannan ya kunshi hular mazakuta (condom), makarin mahaifa (diaphragm), hular bakin mahaifa (cervical cap), hular mazakuta mai sinadarin kashe ‘ya’yan maniyyi (spermicides condom), soson bakin mahaifa mai kashe ‘ya’yan maniyyi (cervical sponge), da sauransu. Laulayin da suke haddasa sune:

a. Bijirewar jiki (allergic reactions). Idan jikin mace ya bijirema wani makarin da tayi amfani dashi, to, canzawa zuwa ga wani makarin daban zai iya magance laulayin.

b. Cututtukan mafitsara (urinary tract infections). Idan akayi amfani da makari wajen yin tazarar haihuwa, to, dole ne mace ta tabbatar da tsabtar gabanta, musamman idan tayi fitsari, ko, kafin yin jima’i, ko bayan gama jima’i, ko lokacin da take yin al’ada. Hakan shine zai rabata da laulayin yin amfani da makarai din. Idan kuma ta kamu da cututtukan mafitsara, sai yaje asibiti domin a dorata akan maganinsu.

  1. Yanke bututun kwan haihuwa (sterilization): wannan hanyar yin tazarar haihuwa ce ta din-din-din, ma’ana ya har abada, domin idan akayiwa mace tiyatar yanke bututun kwan haihuwa (fallopian tube), ba za’a iya mayarda shi ba. Laulayin da yake haifarwa sune:

a. Jin zafi a mara ko ciki bayan anyi tiyatar yanke bututun fallopian tube din (post-operative pain). Za’a iya magance shi ta hanyar yin amfani da magungunan kashe radadi (over-the-counter pain relievers).

b. Yin nadamar aikin tiyatar (post-operative regrets). Yawancin matan da sukaje akayi musu tiyatar yanke bututun fallopian tubes sukanyi nadama daga baya, domin mai yiwuwa ne su bukaci haihuwa daga baya. Idan hakan ya faru, to, abinda kawai za’a iya yi musu domin samun saukin damuwa shine maganganun kwantar da hankali (counseling).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *