YADDA ZAKIYI COCONUT RICE DA MIYAR STEW

Abubuwan bukata

 • Rice
 • Coconut milk
 • Carrot
 • Pies
 • Green beans
 • Tomato, attaruhu, albasa, tattasai
 • Curry
 • Dandano
 • Gishiri
 • Mai
 • Nama

To da farko zamu dauko kwakwarmu sai mu fasa shi mu kankare wannan bakibakin bayan nashi inmun gama kwakwarmu tazamo fara tas sai mu yayyankashi musamishi ishashshen ruwa yadda zaiyi laushi sai muyi blanding dinshi inyayi laushi sai mujuyeshi mutace sai mu ajiye ruwan a gefe sai mu dauko shinkafarmu muyi perboilin dinshi shima mu ajiyeshi a gefe sai mu kawo carrot dinmu green beans da Kuma pies dinmu mu yayyankasu shima musakashi a gefe sai muzo muyi blanding kayan miyan mu suma mu sakasu a gefe sai mu kunna wutar mu mutafasa namar mu da tafarnuwa da albasa da Kuma dandanon mu inmuntafasa sai musauke sai mu dauko tukunya mu daura a wuta muzuba Dan ruwan dumi bamai yawaba yanda inkika zuba ruwan kwakwanki zaiyi daedae yanda shinkafarki bazata cabeba sai kikawo ruwan kwakwan shima ki zubashi akan ruwan duminki sai kikawo Dan gishiri kadan kisa sai kirufe shi inyayi zafi sosae ya dauko tafasa bawae sai ya tafasa ba inkikaga ya kusan tafasane kawae sai kidauko shinkafarki kizubashi a ciki sai ki dauko carrot,pies da green beans dinki suma ki zuba sai ki dan juyasu sai ki rufe shi inyayi sai ki kwashe shinkafarmu ta gamu sai kidauko tukunya kizuba mai ki soya namar ki inyasoyu sai mu kwashe mu dauko kayanmiyar mu muzuba musoya shi da dandanon mu musa Curry da Dan tafarnuwa sai muyita soya shi inyakusan soyuwa sai mudauko namar mu muzuba sukarasa tare inmiyarmu ya soyu shikenan sai mu hadata da shinkafarmu sai ci uwar gida karki bari a baki labarin dadin wannan girki uwar gida dafatan zaki gwada don jindadin mai gida

One thought on “YADDA ZAKIYI COCONUT RICE DA MIYAR STEW

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *