YADDA ZAKI MAGANCE CIWON MARA DA KANKI :

Ga matar da take fama da ciwon mara musamman lokacin al’ada, ko idan zai zo yana zuwa da ciwon mara, wata ma zakaga hattana birgima a kasa, ko taji kamar ana soka mata wuka, ko rikicewar haila, ko jinin ya rinka zuwa da wari, ko karni, ko baki, ko yana zuba sosai to sai a samu: garin gwaiba rumzali na asali lemun tsami ruwa lita biyar (5lrt) sai a dafasu a rinka sha karamin kofi sau biyu (2) a rana za a’samu nasara insha Allah.

DOMIN TSAFTACE MAHAIFA

ga mai bukatar tsaftace mahaifarta da kuma karramata da kashe duk cuta ko kwayar cuta dake zama bakin mahaifa, to wannan hadin da zamu yi bayani yanada muhimmanci musamman ga mai zafin mahaifa, ko kuma yara suna mutuwa a ciki, ko mai fama da toshewar bakin mahaifa ko kuma matsalar ta farune sakamakon amfani da wadansu magunguna na hana daukar ciki ba bisa ka’idaba, ko sha wasu miyagun kwayoyi, ko kuma yawan zubar da ciki, kuma hakan yana iya faruwa idan aka samu mace mai yawan bin maza,hakan zai iya haifar da kamuwa da manyan cututtukan da zasu iya lalata mahaifar.

  • ganyen gwaiba
  • ganyen lemun tsami
  • garin rumzali
  • nana shayi
  • kananfari rabin gwangwani
  • ruwa lita biyar(5lt)

sai a hadasu wuri daya a dafasu, sai a tace idan antace sai a rinka shan karamin kofi sau biyi a rana safe da yamma, zai wanke mahaifa da tsaftaceta da kuma kasha duk wata kwayar cuta da zata iya shiga cikin mahaifa ta kawo illa ga lafiyarki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *