YADDA ZAKI HADA MAGANIN YA MUSHEWAR NONO SU CIKO DA YADDA ZAKIYI MAGANIN KARIN HIPS KIYI ‘YAR DUMA-DUMA

HADI NA FARKO

 • Aya
 • Gyada
 • Agada(plantain)
 • Madara.

Yar uwa ki wanke ayarki sai ki hada da gyada ki markada su ki tace Dama kin rigada kin yanka plantain kin busar dashi kin mai dashi gari kin kuma tankade
Sai ki dinga diban garin nan kina hada wa da madarar ruwa ki dinga sha.

HADI NA BIYU

 • Madara
 • Albasa
 • Garin gero
 • Zuma.

Ki yanyan ka albasarki sai ki sa a tukunya da ruwa ki tafasa ,sai ya tafasa sosai har ruwan ya canza launi zuwa baqi Sai ki juye ruwan a kofi sannan ki dauko zumar ki mai kyau ludayi daya da garin gero ludayi daya da madarar ruwa guda daya sai ki juyesu dika a cikin tafasashen ruwan albasan nan kina sha
Amma fa yar uwa wani hanzari ba gudu ba yar uwa karki bari ya wuce awa ashirin da hudu baki shanye hadin ba.

HADIN KARIN HIPS

Yar uwa ki samu:

 • Abarba
 • Lemu
 • Ayaba
 • Gwanda
 • Kankana
 • Zuma
 • Madara ruwa ta Peak.

Yar uwa ki mar kadasu sai ki zuba zuma da madarar peak ki dinga sha da safe Yar uwa ki samu dankalin turawa ki dafa sai ki bari ya sha iska ki dama shi da madarar shanu ko nono kisa zuma ki yina kina sha cikin wata daya hips zasu fito idan Allah ya yarda

GYARAN NONO‚Äč

kamar yadda kika Sani kowacce mace akwai yanda tsarin halittarta na nono yake.

AKWAI MACE MAI CIMAR NONO.‚Äč

AKWAI MACE WADDA BATA DA CIKAR NONO.‚Äč

yadda danganta da irin tsarin da halitta take.

mace mai girman jiki ( kiba) Zaki sameta da manya nono.

mace mai siranta Zaki sameta da karamin nono.

To daga lokacin fa nono yake lalacewa daga lokacin da mace ta haihu musamman haihuwa farko.

Haka kuma akan sami mace mai gangar jiki amma nono ta karamin.

Ko ki ga mace siririya nononta manya.

To wannan kuma ya samo asali daga gadon da tayi daga bangaren mahaifa.

Idan ya kasance yan uwa mahaifinta mata suna da manya nono to itama zata iya kasancewa mai manya nono.

To idan kika kasance mai daya daga ciki wadannan kina kuma bukatar gyara to ga hanyar.

MAI MANYA NONO‚Äč

Idan kina da manya nono kuma kina so ki rage girmashi sai ki samu Riga nono wacce bata Kai girman wacce kike saka wa ba amma ( gardle) Sannan ki daina cin wadannan abubuwan.

 • gyada‚Äč
 • lipton‚Äč
 • kantu‚Äč
 • kitse‚Äč
 • ki rage shan mangyada‚Äč
 • bota‚Äč
 • man shanu.‚Äč

Idan kika rage ci da shan wadannan abubuwan ko ma ki dauki lokaci ba kya ci, to hakika girmansa zai ragu.

Haka Zaki ci gaba da yi har sai yayi dai-dai ( size) din da kike so Sannan koda Zaki ci sai ki ci kadan yadda ba zai sa nono ya Kara girma ba.

MAI KARANCIN NONO TANA SO YA KARA GIRMA‚Äč

zata nemi wadannan abubuwan:

 • gyada
 • bota
 • romon kaza
 • kayan marmari
 • kantu
 • madara & banbita
 • man shanu
 • madarar shansu da aka tatso
 • kifi

Idan kina so ki Kara girmansa nonon sai ki yawaita cin wadannan abubuwan a koda yaushe Zaki ga nono yana cikowar haka kuma Zaki iya yin wannan gyara koda kuwa bayan kin haihu .

CIKOWAR NONO‚Äč

 • man shanu
 • kwai
 • madarar shanu

Zaki fasa kwai ki zuba mishi madarar shansu sai ki soya da madara shansu kici kullum dare.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *