Akwai dabaru da hikimomi, hadi da kissa da kuma kisisinan da mace zata iya amfani dasu domin ganin ta cusawa mijinta kaunarta a zuciyarsa. Irin wadannan dabaru ba wani wuya ko wahalar gudanar wa suke da shi ba. Sai dai mata da dama basa iya aiwatar da irin wadannan dabaru.
Ga wasu dabaru na yadda zaki kara soyayar mijinki cikin Suki, ba tare da wani sihiri ko tsubbu ba.
Wanka Tare- ba duk mata sukasan cewa yin wanka tare da miji yana kara dankon soayya ba.
Koda kuwa ke baza kiyi ba, to ki yi kokarin ganin kin cuda shi kin wanken shi kamin shi ya daureye kansa. Wannan salon dabaran mallakar miji yana da tasiri matuka ga duk macen da zata saba yiwa mijinta hakan.
Girki na musamman- yiwa namiji girki na musamman da kikasan yana so shima wani salo ne na mallakar miji cikin sauki.Kada kiji kyashin kashe abunda yafi abunda ya baki na hada wannan abinci. Duk macen da zata yi amfani da wannan dabaran na girki zata cusawa mijinta kaunarta cikin sauki, Insha Allah.
Cin abinci Tare- cin abinci Tare- da mijinki shima wani salo ne na mallakar miji.
Koda miji yana cin abinci da abokai ko ‘yan uwane, ki rika samun wani abinci ko kayan kwalama na musamman da zaki rika3 bashi a lokacin da kuke ku biyu kuci tare.
Gaisuwa cikin ladabi- ki zamo mace mai gaida mijinta cikin ladabi duk safiya idan kun tashi. Haka kuma ki zama mai masa maraba cikin kauna idan ya dawo daga aiki ko kasuwa. Ki kasance mai masa fatan akhairi a lokacin da zai fita nema ko aiki.
Kada ki zama mai Mita- Yawan mita ga miji nan take kike fita daga zuciyar namiji. Ki zama mace mai bari magana nan inda aka yita, ba tare da kin ci gaba da mita ba akan abunda ya wuce.
Kada ki zama mai zafin kishi- wasu matan na dauka cewan idan suka nunawa namiji zafin kishi zai sa ya sota, sam ba haka bane. Mata masu zafin kishi akasarin su suna rasa aurensu saboda wannan kishin nasu. Mu hade a part 2.