YADDA XAKI SARRAFA AYABA TAYI MIKI MAGUNGUNA DAYAWA

YADDA XAKI SARRAFA AYABA TAYI MIKI MAGUNGUNA DAYAWA

Ita Ayaba ba tuwonta kadai yake da amfani ga jikin dan adam ba hatta bawonta in kuka duba abubuwa ne masu dama a ciki

Yana da Potassium mai dama ga Fibres wasu nan da nan suke narkewa wasu kuwa ba sa narkewa wannan ya sa niqe abinci yake zama abu mai sauqi a wurin hanji

Bawon Ayaba yakan taimaka wajen rage yawan Cholesterol mara amfani a cikin jini da haka sai hatsarin kamuwa da cutar zuciya ya ragu

Bawon Ayaba na tattare da sinadarin Tryptophane wanda ke qara yawan sinadarin sanya qwaqwalwa nashadi da qarin sakewa wato Serotonin

Yana da kuma Luteine wanda shi daya ne daga cikin manyan Antioxidants masu taimakawa wajen lafiyar ido da maganin wasu cututtukan

Matammu ma a Nigeria ba wani sabon abu ba ne wajen yin amfani da bawon Ayaba don gyaran fata kamar yadda Khadija Abdulkadir ta fadi ba shakka akan bare Ayaba a manna bawon nata ta ciki a fuska ko a goga a duk fuskar sai a bar shi na kimanin mintoci sai a wanke da ruwan dumi yakan qara laushin fata ya kuma yi maganin tattara

Bawon na Ayaba yakan taimaka wajen rage qaiqayin fata ya magance gurabun cizon qwari kamar sauro ko kudin cizo har da radadin fata na ba gaira ba dalili yana kuma qunshe da Antibacterial wanda yake magance qurarraji masamman na kan fuska

Akan yi amfani da bawon kuma wajen sanya takalma da jakunkunan fata su yi haske da walqiya har ma da kayan ado na azurfa

Akan yi amfani da bawon Ayaban wajen sassauta radadin ta wajen shafa bawon kai tsaye a wurin na dan wani lokaci nan da nan zai shiga ciki ya kau da radadin cikin lokaci

Bawon Ayaban kan taimaka wajen hidda siririyar qaya a fata sinadarorin dake tattare da bawon za su taimaka sai qayar ta fita ba tare da wata wahala ba kuma ba wani radadi

A lokacin da mutum yake fama da ciwon kai sai ya sami bawon Ayaba ya shafe goshinsa zuwa wuyayensa in sha Allahu radadin zai yi qasa

Sannan akan yi aiki da shi don haskaka haqorabarin ciki din ne za a yi ta goge haqoran da shi har dai su yi haske

To ba shi kenan ba ita ma fa ba ta rasa nata matsalolin matuqar mutum ya wuce haddi a kanta

Don mugun cin Ayaba zai iya tsawaita qwayoyin jini a qarshe mutum ya qare da ciwon kan gefe guda

Haka in aka ci ta da yawa in dai ba a sha ruwa sosai ba za a iya kamuwa da kumburin ciki zuwa atini ko zawo

Koda yake muna tunanin cewa ba ta qara qiba amma wadan da suke da jiki ya kamata su san yanayin da za su riqa cin ta misali qwara biyu kawai a rana

Yana da kyau a guji cin Ayaba lokacin da za a kwanta don kar mutum ya kasa barci ko ma ya farka ba gaira ba dalili ya kuma gaza komawa

Da yake tana da Potassium sosai in za riqa yawaita ta kowani lokaci ba mamaki mutum ya iya kamuwa da ciwon zuciya

Ba a cewa ta dace da kowa akwai wadan da in suka ci ta sa su yi fama da wasu matsalolin kamar ciwon ciki ko kumburinsa ko zawo ko atini

Zai yi kyau ga wanda ya ci ta ya wanke bakinsa sosai masamman yara qanana don sukarin dake cikinta akwai yuwuwar ta bata musu haqora

Ayaba ba ta da Protein mai dama a cikinta kenan bai kamata mutum ya cika cikinsa da ita wai don yana jin yunwa ta maye masa makwafin abincinsa ba

Yawan cinta kai tsaye ba a juice ba zai iya wahalar da zuciya sai a kiyaye

Masu shayarwa su ma su kiyaye don jaririn zai iya samun matsalar yin ba haya

Ba wai Ayaba kadai ba yana da kyau duk ya yan bishiyannan mu kyautata cinsu wani yakan ci su ne kan jiki kan qarfi don an ce suna magani wani kuwa don dadinsu ne wani sai ya mai da su abin da zai ci na wannan lokacin wani kuwa in ya saya ba zai so ya yi adarar kudinsa ba sai ya cinye to ba shakka kamar yadda aka ce ne abincinka maganinka su a matsayin magunguna suke in mutum ya yi overdose zai iya shiga wani yanayi wanda bai zata ba wasu cututtukan da muke kamuwa da su duk daga abin da muke ci ne sai mu kiyaye

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *