Kayan hadi
- Farar shinkafa ta tuwo
- Backing powder
- Suger
- Yeast
- Gishiri
Yadda zaki hada
Dafarko uwar gida zaki wanke shinkafarki saiki dafa wata daban kihada akan danyar kibayar amarkado miki,saiki sa yeast da suger da backing powder,zaki iyasa gishiri kadan saiki juya kamar dai yadda ake kwabin wainar shinkafa amma kwabin sinasir yafi na wainar shinkafa ruwa,saiki Sa arana in yatashi saiki dauko kaskon suya kisoya mangyada da albasa sabida wani man yanada wari inkikasoya saiki juye akwano,saiki sami auduga maikyau ko brush din girki, saiki dinga dangwalo man dashi kina shafawa a kaskon saiki zuba kullin kirufe kibarshi zuwa yan mintuna saiki cire ba ajuya sinasir haka zakiyi tayi harki gama,sai ayi miya maikyau aci da ita.
Aci dadi lfy