YADDA AKE WAINAR DANKALI

Abubuwan bukata

  • Dankali
  • Kwai
  • Nama (kifi ko sadine)
  • Kayan kamshi
  • Albasa, attarugu ki hadesu kijajjage
  • Mai
  • Inkin kara wani abu ke kika sani

Procedure

Zaki fere dankalinki kiyankashi cube kanana kidan zafkashi se ki aje gefe,se ki aza fry fan dinki ko pot dinki bisa murhu kisa mai dan kadan kizuba namanki wanda kika yanka kanana kizafkashi idan yazafku seki saka jajjagaggen tarugunki da albasa kisa maguna da kayan kamshinki idan kinadasu idan kuma bakidasu wannan matsalarkice ke kika sani ,kisa dan gishiri seki jujjuyasu kibarsu Sudan tananu,seki dauko zafkakken Dankalinki kihadasu ki mommotsa eh nace ki mommotsa idan baki motsaba ke kika sani seki sauke hadinki ki aje gefe, seki dauko kwai ki faffasa dafa dan yawa sbd anaso hadin yayi ruwa ruwa ki kaÉ—a kisa maggi da Black pepper (masoro) don rage kanni se ki dauko wannan hadin naki ki zuba cikin kwan ki mommotsa ki daura tandarki bisa wuta kisa mai kizuzzuba wannan hadin naki ki rufe yadan dahu se ki bude kijuya ki barshi bude yasoyu
Hikimar anan itace idan kika rufe bazeyi ruwaba tsaka tunda ƙwaine zafi ke dafa shi so shikenan kingama

Se kaiwa Oga kodayake imma kwata zaki almajirai zaki ba ke kika sani
Namaki me wuyar tunda nakoyar idan kin iya ke kika sani

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *