Yadda ake sinasir din alkama

Abin da ake bukata

  • garin alkama
  • yeast
  • gishiri
  • suga
  • ruwa
  • kwanon gashi
  • filawa

Dan Allah kuyi share

Yadda zaa hada

Asamu kwano azuba garin alkama kofi 2 akawo filawa babban cokali 2 ko 3 azuba, akawo qaramin cokali na yeast azuba sai azuba suga qaramin cokali sai gishiri kadan.
Sai akawo ruwa mai dimi akwaba. Kwabin ayishi da kauri bayan an kwaba sai a rufe ya tashi. Idan ya tashi sai asamu ruwa kadan azuba ciki sai asa abin motsawa jujjuyashi/motsa
Sai a dora tukunyar gashi /fryin pan a wuta matsakaici, idan fryin pan naki na kamu ashafa mai kada aciki kafin azuba kullun idan ko baya kamu ba sai anshafa mai ba. Sai azuba kullun abarshi har yayi kwayakwai/bobbles har kuma su fashe sai ajuya dayan gefen shima agasa har duka gefen suzama light brown. Sai a kwashe akuma zuba wani har aqare gabadaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *