YADDA AKE SARRAFA DANKALIN TURAWA TA HANYOYI DABAN_DABAN

Content:

Awara da dankali
Potato balls
Potato cake
Dadin Potato
Potato Soup
Potato Crush.

AWARA DA DANKALI
Ingredients
Dankali
Onions
Pepper,
Maggi,
Salt,
Thyme
Ki sami dankalin turawa ki gurzashi a grater, sai ki tsame shi ki zuba a kwano me kyau, sai ki yanka albasa ki jajjaga attaruhu ki zuba akan gurzajjan dankalin, kisa magi, gishiri, tym, sai ki fasa kwanki akai, ki juya sai ki sami farar leda ki zuba ki dora awuta, ya dahu, sai ki yanyanka kamar awara, sai ki dinga tsomawa a ruwan kwai kina soyawa aruwan mai. aci dadi lfy

POTATO BALLS
Ingredients
Pepper,
Albasa,
Eggs,
Flour,
Maggi
Yadda Ake Hadawa
Da farko dai za’a samu dankali mai kyau a fere shi sannan a wanke shi, sai a samu attarugu ko tattasai da albasa sai a dake su sai sun daku, sai a dauko irish din da aka riga aka fere sai a samu grater a rika goge irish din kaman yanda ake goge goro, daga nan sai a dauko attarugu da albasa can da aka riga aka dake sai a hade shi da irish amma a tabbatar irish din bai da ruwa ko kadan daga nan sai a samu kwai guda daya a fasa aciki sai fulawa a sa, sannan magi duk irin wanda ake so, amma a tabbatar ba’a sa ruwa ba kwai guda kawai ya isa daga nan sai asa spoon a motsa sai a aza mai a wuta a bari yayi zafi sai a dinga diba ana toyawa kamar yadda ake toya kosai.

POTATO CAKE
Ingredients
Dankali,
Egg,
pepper,
Onions,
Oil,
salt
Yadda Ake Hadawa
A yayyanka dankali kanana kada a dafa a barshi a danyen shi, yankan kamar girman sweet ko kuma yaddda ake yanka koda, sai a yanka tattasai da albasa a zuba akan dankalin har da magi da gishiri idan an kammala sai a sa mangyada kadan cikin kwanon tuya idan yayi zafi sai a zuba su dankalin nan. Mu fasa kwai mu kada mu zuba a bisa dankalin ya hadu a rufe ruf har sai dankalin nan ya dafu, kada a cika wuta

DADIN POTATO
Ingredients
Dankali
Meat,
Peas
Green beans,
Carrots,
Curry,
garlic,
Maggi,
salt,
pepper
Yadda Ake Hadawa
Ki samu naman ki mai kyau mara kitse,ki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *