YADDA AKE PEPPER CHICKEN

Abubuwan buqata

  • Kaza (ta turawa)
  • Albasa me Lawashi
  • Spices
  • Gishiri
  • Tandoori spc(Optional)
  • Kitchen spice
  • Citta
  • Tafarnuwa
  • Maggi
  • Tattasai
  • Taruhu
  • Mai

Yadda ake hadawa

Da farko dai ya kasance kin wanke kazanki tas kin cire mata duk wani datti, Ki zubata a tukunya ba tare da kinsa mata ruwa ba (kunsan kajin turawa basason ruwa sosai). Kiyanka albasa mai yawa tare da lawashinta ki zuba a kai dan ki tafasa kazar, ki sa seasonings da spices na ki, ki sa gishiri da tandoori Kitchen spice da Kuma citta da tafarnuwa duk don ki cire karnin kazar ki, ki rufe ki bata minti 10 don ta tafasa. Ki juya don maggi ya ji ko ina, Ki zuba a wani bowl asa man gyada ya yi zafi sosai sai a soya wannan kazar har sai kinga ta yi ja sosai dan ta yi dadi, za kuma tafi dadewa a ajiye, ba kamar in kin soya ta ne sama sama ba. Bayan kin gama soyawa, sai ki rage mai kadan ki zuba chopped tattasai da Taruhu, ki sa albasa da lawashi, sai seasoning na ki, ki tabbatar ya ji albasa sosai, sai ki soya sama sama kamar 10min sai a sauke. A karshe, sai ki juye sauce din a cikin soyayyar kazar ki Aci dadi lfy

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *