YADDA AKE MIYAR WAKE

Kayan Hadi

  • 1 cup beans
  • manja
  • tarugu albasa
  • nama
  • tattasai
  • tumatur
  • cube seasoning
  • garlic
  • ginger

Yadda ake Hadawa

Zaki wanke wake kamar zakiyi moimoi ki dora a wuta yafara dahuwa

Kiyi grating din kayan miyanki da ginger da garlic

Idan wakenki yayi seki dora wata tunkuyar kizuba manja kisa.albasa idan yafara soyuwa seki zuba kayan miyan

Ki zuba seasoning da spices dinki ki juya sosai seki juye waken akai kidan kara ruwa kadan kisaka namanki da kika gyara kika soya kirufe ya dahu sosai idan yayi zakiji yana kanshi

Seki sauke zaki.iya ci da tuwon shinkafa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *