YADDA AKE KARA KWAREWA A WAJEN GIRKI

Kowanne mutum yana so ya kware a fannin da yake. Shima girki ana bukatar kwarewa a lokacin da ake yinsa. Koda ace kina tinanin cewa bazaki iya kwarewa ba, ti muna fatan wannan tinanin zai chanza. Kamar yadda ake koyar komai, ana bukatar naci, gwaji da kuma neman ilimi. Kawai ki kwantar da hankalinki amma ki dauka cewa wasa kikeyi da kayan hada abincin zaki fahimci cewa girki abu ne mai sauki.

  1. Ki nemi kari akan abinda kika iya

Neman karin ilimi yana da kyau domin kuwa kin riga kin iya kananun abubuwa na girki kawai kina so ki kware ne. Ki siyi litattafan girki sannan kuma ki dinga kallon bidiyo na girkie-girke, ki karanta ko da ace kin riga kin iya kalar girkin. Musamman abincin mu na hausawa, akwa kala-kalar yadda ake girka abinci kala guda daya, saboda haka, akwai sabon abu da zaki iya koya.

  1. Lokaci

koda ace kin san kayan da ya kamata da ki girka abinci dasu, yana da kyau ki san lokacin daya kamata ki zuba kowanne kayan hadin.

  1. Tsarawa

Akwai abubuwan daya kamata mutum ya tanada tun kafin a kunna wuta a risho ko murhu. Misali, zaki iya daukar lokacinki wajen yayyanka duk kayan miya da zakiyi amfani dasu wajen girkin, ki zuba kowanne a roba daban sannan ki ajiye a gefe. Hakan zai taimaka saboda da zarar lokacin zubawa yayi kawaai daukowa zakiyi ki zuba.

  1. Lura da dukkan bayanai

Ki kula da yadda kike kara kwarewa daga farko, tsakiya har ma zuwa karshe. Haka zalika, ki lura da yawan wuta da kike buka domin yin girki. Hakan yana taimakawa ki san abincin da yake bukatar wuta sosai da kuma wanda ma baya bukata.

  1. Ki tanadi kananun abubuwa da kike bukata

Akwai abubuwan da kanana ne amma kuma dole ne ana bukatarsu wajen yin girki. Misali anan kamar wuka, chopping board domin zasu taimaka wajen yin aikin ki sosai sama da idan baki dasu.

  1. Yin shiri

Yana da kyau ki shirya abinda kike so ki kara kwarewa wajen girka shi tun kafin lokacin yazo. Hakan zai sa ki sayi duk abubwan da ake bukata kafin lokacin girkin.

  1. A lura da lokaci

Idan ana so a kware a girki, anfi so dinga yinsa idan babu abubuwa masu dauke hankali sosai. Kar ki fara girki idan ana wani fim da kike so a TV ko kuma ana wani shiri a radiyo. Idan babu abubuwa masu dauke miki hankali, zaki tattara hankalinki ne zuwa wannan girkin ne.

  1. Bawa kai lokaci

A ko yaushe ki dinga kanki lokaci sosai. Ba rana daya ake kwarewa wajen girki ba, ana bukatar lokaci. Misali, yawan gwaji zai nuna miki ainihin lokacin da zaki dauka wajen girka farar shinkafa kafin yaran makaranta su dawo. Haka zalika, idan kin gayyaci mutane gidanki ba sai kin dinga shiga kitchen kina fitowa ba a maimakon ki zauna kuyi hira.

  1. ki kirkiro abubuwa

Ki tina cewa gidanki ne, kuma kitchen dinki ne. Saboda haka kina da damar gwada yin wasu abubuwan kamar soya kayan miya ba yadda aka koya miki ba, idan kinji yayi dadi kinga kin gano wani sabon salon. Idan kina tinanin akwai daya daga cikin kayan hadin da kike so ki cire, zaki iya cirewa domin ki ji yadda abincin zai kasance.

  1. Gwaji

Akwai banbanci tsakanin macen da take girka taliya duk ranar juma’a da kuma wadda take girkawa duk bayan watanni biyu. Saboda haka, ki dinga gwadawa sosai domin samun kwarewa.

Da fatan wadannan abubuwan dana ambata zasu taimaka wajen kwarewa a girki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *