Wannan hadin yana sa mace ta kasance cikin ni’ima da yawan naso matukar tana shan wannan hadin kuma wanda suke shan wannan hadin ba a kwace musu miji kema ki koya kiga yanda zaki tara ni’ima.
Zaki nemi kayan hadin kamar haka;
- Kankana
- Garin kanunfari
- Garin dabino
- Kwakwa
Madara ta Ruwa
YADDA AKEYIN HAÆŠIN
Bayani; Zaki samu kankana mai kyau sai ki fere samanta kiyi mata kofa a sama sai ki kawo garin kanunfari ki zuba a cikin kankanar sai ki samu garin dabino shima ki zuba a cikin kankanar sai kuma Kwakwa kwallo daya ki fasa ki zuba ruwan a cikin kankanar sannan itama kwakwar ki gurzata ta zama gari ki zuba aciki kankanar shikenan kin hada sai ki ajiyeta a waje mai tsafta kamar firige bayan awa goma sha biyar (15 hours) sai ki fara sha harya kare, yar uwa wannan hadin ba na bari bane ,na musamman ne