Yadda Ake Hadin Garin Sha’ir Don Motsa Sha’awa:

Zaki nemi kayan hadi kamar haka;

 • Garin sha’ir
 • Garin alkama
 • Garin dabino
 • Garin shinkafan tuwa
 • Nonon akuya

Zaki samu wadannan kayan hadin sai ki hadesu guri guda ki gauraya ki dunga sha da nonon akuya.

Yadda Ake Hadin Sassaken Baure Don Karin Ni’ima:

Zaki nemi kayan hadi kamar haka;

 • Sassaken baure
 • Garin kanunfari
 • Mazarkwaila
 • Garin cotta
 • Garin minannas
 • Zuma

Zaki samu sassaken baure ki tafasa idan ya tafasa sai ki sauke ki tace ruwan ki maida ruwan kan wuta sai ki zuba saurin kayan hadin ki dafa sosai sai ki sauke sai ki kara tacewa ki maida shi ruwan shanki.

Yadda Ake Hadin Lubba Zakari Don Rage Kiba:

Zaki nemi kayan hadi kamar haka:

 • Lubban zakari
 • Garin Ganyen shayi Dan aune
 • Garin habbatus sauda
 • Sugar
 • Zuma

Zaki samu wadannan kayan hadin ki hadesu guri guda ki tafasa ki tace ruwan ki sa sugar ki kuma zuba Zuma a cikin ki juya sai ki dunga diba kina sha, in sha Allah zai rage.

Yadda Ake Hadin Kyauta Bashiri:

Yar uwa wannan hadin yana da matukar mahimmanci yana saurin saukar da ni’ima kuma yana sa mai gida yaji wani dandano na musamman.

Zaki nemi kayan hadin kamar haka;

 • Kokumba
 • Tuffa (Apple)
 • Garin albabunaj
 • Garin citta
 • Madara peak

Zaki samu kokumbanki mai kyau ki yanka kanakana sai tuffanki itama ki yanka sai ki hadasu ki markada sai ki zuba garin citta da garin albabunaj sai ki juya sai ki barshi ya jika tace sai ki zuba madara sai ki dunga sha tundaga rana har dare.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *