YADDA AKE HADA SABULUN ZUMA (HONEY SOAP) CIKIN SAUKI IN SHAA ALLAHU

Abubuwan buqata

  • Caustic soda gwangwani daya
  • coconut oil gwangwani uku
  • zuma rabin gwangwani
  • turare of your choice essential oil

Dafarko zaki auno Caustic soda gwangwani daya sai ki jika shi da Ruwa gwangwani biyu ki juya shi har sai ya narke sai ki barshi zuwa awa 24hrs

Bayan yayi awa 24hrs sai ki dauko coconut oil dinki gwangwani 3 ki zuba a roba Mai Fadi ko girma idan ya daskare sai ki fara narka shi idan kuma bai daskare ba shi ke nan,Bayan kin zuba coconut oil a roba sai ki dauko wannan Caustic soda da kika jika ki zuba akan coconut oil din sai ki ta juyawa har sai ya hade jikinsa kin dena ganin alamar mai Zakiga yayi kauri,xaki Dade kina juyawa kafin ya narke.

Bayan nan sai ki dauko zuma rabin gwangwani ki zuba kita juyawa again daganan saikisa masa turare saiki sake juyawa, shike nan sai ki zuba turare,seki sakaa color kijuye a mold saiki rufe shi zuwa awa 24,sai ki Bude Ki barshi ya bushe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *