Baya ga masu sha’awar samun kayan marmari na ’ya’yan itatuwa, wasu sun fi son abin sha da aka hada ’ya’yan itatuwa domin kara lafiyar jiki da kara kuzari
Shi ya sa muka kawo muku yadda ake hada ‘juice’ din kayan wadannan kayan marmari, wato abarba da kankana domin samun ingantacciyar lafiya
Kayan hadi
Kankana
Abarba
Suga mazarkwaila
Flavor
Yadda ake hadawa
A samu abarba a wanke sai a yayyanka shi a dora a wuta tare da suga mazarkwaila. idan ya tafasa sai a sauke
Bayan ya huce sai a yanka kankana a hada da abarbar a markada,
Daga nan sai a tace a zuba flavor daidai bukata
Sai a sa a fridge yayi sanyi
A jaraba wannan hadi aga aiki ajiki
A turawa yan uwa su amfana