Yadda Ake Hada ‘Juice’ Din Kankana Da Abarba don Karin Lafiya

Samun abu mai dadi a lokacin bude baki abu ne mai bukata musamman abin sha mai dadi.

Baya ga masu sha’awar samun kayan marmari na ’ya’yan itatuwa, wasu sun fi son abin sha da aka hada ’ya’yan itatuwa.

Shi ya sa muka kawo muku yadda ake hada ‘juice’ din kayan wadannan kayan marmari, wato abarba da kankana.

Kayan hadi

Kankana
Abarba
Sukari
Flavor

Yadda ake hadawa

A samu abarba a wanke sai a yayyanka shi a dora a wuta tare da sukari, idan ya tafasa sai a sauke

Bayan ya huce sai a yanka kankana a hada da abarbar a markada,
Daga nan sai a tace a zuba flavor daidai bukata

Sai a sa a fridge yayi sanyi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *