Girke-Girken Azumi
Gurji/Cocumber, da Na’a-na’a nau’in kayan abinci ne da suka ƙunshi sinadarai masu amfani sosai ga lafiyar jikin ɗan Adam.
Cocumber na ɗauke da wadataccen ruwa a cikinsa, da ke taimakawa wajen rage ƙiba da bai wa jiki ruwan da yake buƙata.
A hannu guda kuma na’a-na’a na taimaka wa jiki magance matsalolin magwas da kumburin ciki tare da taimaka wa ƙwaƙwalwa da kuma hana warin baki na larura.
Kenan haɗa Waɗannan abubuwa biyu a waje guda, ba ƙaramin lafiya zai ƙara wa jiki ba.
Kayan hadi:
- Na’a-Na’a
- Cocumber
- Dafaffen sukari/Syrup
- Filebo
Yadda ake yi:
Da farko a samu Na’a-na’a koriya sosai sai a wanke ta tas.
Sai a markaɗa ta daga nan sai a tace a ajiye ruwan a gefe guda.
A samu Kokumba mara daci a yayyanka ta a markaɗa a tace.
Sai a dafa sukari har sai ya narke ya zama tsararo (syrup).
A juye tattaccen ruwan Na’a-Na’a da na Kokumba a kofi.
Daga nan sai a ɗauko syrup din a zuba a kan haɗin.
A zuba filebo na ruwa, ɗanɗanon da ake so, a ciki.
Sai a sa a fridge, ko a jefa ƙanƙara a ciki, idan ya yi sanyi sai sha