Yadda ake gyaran jiki da madara da kuma lemon tsami

Shi wanna hadi yana qara wa jiki kyau da kuma haske idan ana yi akai akai. yadda ake yin wannan hadi shi ne

A samu madarar gari, a jika kadan da ruwa sannan sai a matse lemon tsami a ciki, a gauraya sosai sai a shafe fuska da hannu dama duk inda ake da bukatar yayi haske da laushi ko da duka jiki ne za a iya shafawa. Wannan hadi idan ana yin shi akai-akai za a ga yadda jiki zai yi kyau, laushi da kuma haske. Bayan an shafa, sai a barshi na tsawon minti biyar, sannan a wanke da ruwan dumi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *