Yadda Ake Anfani Da Hulba Waja Gyaran Breast

hulba don gyaran nono. Dalili kuwa shine, hulba na sanya fata da tsokar dake kewayen nonon mace su buɗe, hakan sai ya sa nonon ya ciko ɓulɓul abin sha’wa, musamman idan nonon ya kasance da girmansa amma ya kwanta.

Abubuwan da ake bukata sune; garin hulba da garin Shammar da kuma zuma.

Yadda za a hada.

Za a samu garin hulba da garin shammar. Ki ɗebi cikin ƙaramin cokalin guda daya (1) na garin hulbar sai a zuba cikin kofi mai tsafta da aka tanada , sannan a zuba garin shammar, shima cikin ƙaramin cokali guda, sai a gauraye su waje guda. Daga bisani a dafa ruwa idan ya tafasa sai a kwara a kan garin hulba da na shammar dake cikin kofin a juya su da cokali, bayan haka sai a rufe kofin. Bayan kamar minti 10 sai a tace da rariya, bayan an tace, sai a kawo zuma mai kyau a zuba a sha.

Daga bisani sai a shafa man hulba ga nonon. Wajen shafawa akan nonon a tabbatar an murza man hulbar sosai akan nonon gaba daya yadda zai shiga fatar nonon da kyau. Za a sha wannan hadin sau biyu a rana, wato da safe da kuma dare, kuma duk lokacin da aka kammala shan shayin hakanan za a shafa man hulbar a kan nonon, shi ma ya zama sau 2 kenan.

Yadda za ki gane maganin na amfani shine, ta hanyar jin nononki na kara nauyi, alamar ya fara cikowa kenan. Allah Ya sa mu dace,amin.

Karin Bayani: A inda mu ka ambaci amfanin hulba ga lafiyarmu, amma ba mu yi bayanin yadda za ayi amfani da ita ba, to mu na nufin mutum ya ke amfani da kwayoyin hulbar a abinci, ko kuma ya rinka yin shayinta ya na sha.

Idan a shayi mutum ke son amfani da hulba, sai ya ke shan kofi daya na shayin sau 2 a kullum, wato da safe da kuma dare

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *