Yadda Wata Tsaleliyar Budurwa Kyakkyawa Take Neman Mijin Aure ruwa a jallo hakika wannan zamani da muke ciki yazo da irin wasu abubuwa masu sarkakiya akan yan matan mu na hausawa cewar budurwa mai neman mijin aure a shafin sada zumunta.
Babu shakka yarinyar ta kasance son kowa kin wanda ya rasa, idan akayi duba da kyawawan hotunan ta data turowa shafin gidan jaridar vanguard news, nigeria saidai budurwar ta nemi a sakaye sunanta da kuma fuskar ta.
Budurwar wacce ta kasance Bahaushiya ce, amma tana zama tare da iyayenta a yankin jihohin Yarbawa (Sabo Ibadan), tace tana bukatar mai tsaron Allah kuma wanda yake da sana’a da rufin asiri, ba wai sai wanda ya tara abin duniya ba.
Ga duk mai bukatar son auren wannan kyakkyawar budurwa zai iya tuntubar mu ta comments domin ganin yadda zamuyi kokarin hada shi da lambar ta don samun daidaitawa tsakanin su amma don allah mai sonta da gaske take nema ba wanda yake sonta da wasa ba.
Hakika lokuta bayan lokuta akan iya samun irin wadannan ‘yan mata da suke neman mijin aure ruwa a jallo sakamakon takurar da wasu suke fuskanta a wurin iyayen su ko kuma yayin su, ko kannan su da suke gida daya sakamakon suna ganin su, a gida daya yau da gobe raini yake biyo baya.
Assalamu Alaikum Warahmatullah
Dangane da wadda ke Neman mijin Aure
Daga yankin Yarbawa sabo Ibadan
Shin ko ta samu mijin Auren?