WASU ZAFAFAN SAKONNIN BARKA DA ASUBA DA ZAKU IYA TURAWA MASOYANKU

Yiwa masoyi sakon barka da asuba yakan sa masoyi walwala da natsuwa. Irin Wadannan sakonnin sukan sa namiji ya wuni da tunanin masoyiyarsa.
Ga wasu sakonnin nan:

1: Da fatan masoyina ya tashi lafiya. Kada ka cika sugar a shayin da zaka sha gudun kada zakinka dana sugar su maka illa abun kaunata,. (Na matan aure ne).

2: Da zanyi arba da kai a wannan safiyar da zan rabu da ciwon idon rashin ganinka danake fama dashi.

3: Na kwanta da kewarka. Na kuma farka da soyayyar ka. Wannan yasa nake neman sanin yadda ka kwana ka tashi.

4: Babu abunda ke zuwa mini a rai sai daren karshe kamin kayi tayi. Da fatan ka tashi lafiya. (Na matan aure ne).

5: Da zaka karanci zuwaciyata, zaka fahimci ina tsananin tunaninka a wannan safiyar. Idan bazaka karanci zuciyata ba, ina fatan zaka karanta wannan sakon nawa na barka da asuba.

6: Hotonka dake bango dakin mu shine abunda idanuwana suka soma arba dasu a wannan safiyar. Hakan yake tuna mini irin sa’ar danyi cikin mata na samun miji Irinka. Barka da asuba. (Na matan aure ne).

7: Fadowa daga kan gado danayi shi yasa na fahimci gari ya waye. Sai dai faduwar tawa ya tabbatar mini da zamanka a birnin zuciyata. Da fatan ka tashi lafiya.

8: Gari ya waye, lokaci yayi da zaka tashi ka fuskanci nema bayan gaisawa da Allah (SWT). Kada kuma ka manta da masoyiyarka dake maka fatan Alheri ako da yaushe..

9: Ina kaunarka, amma kuma ina sonka, ina fatan kasancewa tare da kai har abada, ina burin ganin na zama uwar yaranka. Allah Ya bada sa’a idan an fita nema.

10: Ina kwana ga mutumin da yake na farko abun tunawa a zuciyata ako wace safiya. Kuma mai sani farin ciki ako wacce rana.

Da fatan mata zasuyi amfani dasu domin sace zuciyar masoyansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *