- Idon Zakara:- Wata ciyawa ce mai kananan ganye, kuma tana da zaki idan aka tauna.
Ya
yanta suna kama da kwayoyin Dawa amma su kalarsu ja da baki ne, suna kama da kwayar cikin idon zakara. Yana maganin typhoid, maganin zazzabi, yana kara jini, yana rage radadin ciwo sannan yana da kyau wajen abinda ya shafi kwanciyar aure ga mata. Ana iya tafasa ganyen Idon Zakara a sha acikin shayi ko kuma a hada shi acikin kayan yaji. - Nonon Kurciya:- Wata ciyawa ce mai yado a kasa, ganyenta kore ne,tana kwaciya a kasa inda danshi yake. Tana maganin gudawa, cututtukan da ake dauka yayin saduwa, ciwon kansa, dafin kunama, da maganin namijin dare ga mata. Ana busar da nonon kurciya, sai a dinga zuba garin acikin nono ko ruwa ana sha.
- Tubanin Dawaki:- Yana maganin zazzabin Maleria, gudawa, cututtukan kwakwalwa, ciwon ido, ciwon kunne, da saran maciji.
- Qaimin Qadangare:- Wata ciyawa ce, tana dan yo tsayi kadan, tana da kaikayi da `yan kayoyi ajikinta. Yana magance cututtukan fata, maganin gudawa, ciwon hakori na yara, ciwon koda kuma yana maganin matsalolin Aljanu idan aka busar da shi ana yin turare da shi.
- Zaki-banza mai kaya:- Yana magance cututtukan makogwaro, maganin tari, ciwukan kansa, cututtukan fata, kunar wuta, maganin zazzabi da kuma matsalolin numfashi.
- Kashin Yawo:- Yana maganin gudawa, saukake fitowar hakori na yara, ciwon ciki, ciwukan fata da kuma zazzabi.
- Takalmin Binta:- Wani tsiro ne mai fitowa kala-kala, galibi korene da jar fulawa a kansa. Yana kama da `kasan takalmi. Yana maganin ciwon nono.
- Kargon Allah:- Yana magance Matsalolin ciki, ciwukan zuwan jinin al’ada, ciwon koda da kansa da kuma maganin gudawa.
- Rai-rai / Rai-dore:- Yana maganin Typhoid, Maleria, matsalolin mara, hawan jini, tsakuwar ciki da kuma cutar basir.
- Wuyan Damo:- Yana maganin ciwon mara, matsalolin zuwan jinin al’ada da kuma maganin tari.
- Ka-fi-Mallam / Ka-bi-Mallam.
Maganin matsalolin ciki. - mace da goyo yana maganin ciyon hanta da h I v
- Fidda Sartse:- Yana maganin ciwon kafa, ciwon kai da kuma cututtukan da ake iya dauka yayin saduwa.
- Kurar Shanu:- Tana maganin ciwon Kansa da matsalolin fata.
- Bi-ni da zugu:- Maganin yoyon fitsari, cututtukan da ake iya dauka yayin saduwa, ciwukan yayin zuwan al’ada, da kuma cutar typhoid.
- Mikiya:- Wannan ciyawa tana magance ciwon hauka, maganin gudawa, matsalolin fata, zazzabi, ciwon kai da kuma sanyin jiki.
- Ka fi Amarya kamshi:- Wata ciyawa ce mai kama da Na’ana’a, koriya ce mai kamshi. Tana da fulawa mai kalar ja da yalo. Tana kashe dafi, tana maganin ciwon hauka da zazzabin Maleria, tana maganin matsalolin Aljanu.
- Zabuwa:- Maganin ciwon ciki, konewar fata, ciwukan fata, warkar da ciwo cikin sauri, tana kuma maganin ciwukan ido da na kunne.
- Abin kan iyaka:- Yana kara jini, rage matsalar hawan jini, da kuma maganin cizon maciji.
- Fasa Kumburi na mace:- Yana maganin zubar jini, ciwon mara, gudawa, cutar cancer, cututtukan da ake iya dauka yayin saduwa da kuma cutar asthma.
- Fasa kumburin namiji:- Yana magance matsalolin ciki, tari, asthma, yana tsaftace jini, yana maganin ciwon qirji da basir.
- Kai dubu:- Yana magance ciwon Hauka. (mental illness).
- Farin Ruwa:- Yana maganin cutukan sikila da Maleria.
- Qaiqayi koma kan masheqiya:- Yana maganin cizon maciji, maganin gudawa, kuma yana maganin Aljanu da sihiri.
- Kuru-kuru:- Yana maganin ciwon koda da matsalolin ciki kuma yana rage radadin ciwo.
- Goga masu:- Yana kara jini, yana maganin asthma, cututtukan fata, basir, cututtukan da ake iya dauka yayin saduwa, ciwon koda, sikila, tsattsagewar kafa da matsalolin ciki.
- Wuta-wuta:- Tana kashe kwayoyin cuta, tana maganin sikila, tana rage radadin ciwo sannan tana maganin ciwon suga.
- Taba-taba:- Tana maganin ciwon hauka.
- Idon Shanu / Gautan kura:- Yana maganin ciwon Hauka.
Karin bayani
Dukkan wadannan tsirrai ne da ake iya samunsu a kasar Hausa, musamman Arewacin Nigeria, don haka ko ina za ka iya samunsu, wajen masu magungunan gargajiya.
Wadannan tsirrai mun fadi amfaninsu ne kawai
Binciken amfanin wadannan tsirrai, mun yi shi ne akan tsarin Binciken maganin gargajiya ta hanyar zamani don haka fa’idodi ne da aka tabbatar da su ta hanyar binciken likitanci na zamani.
Allah Ya sa mu dace Aamin