WASU DAGA CIKIN AMFANIN MAN RIDI WANDA YAKAMATA KUSANSU
- Gyara fata da inganta lafiyar ta.
- Kara girman gashi da launin bakin sa.
- Kariya daga ciwon-daji (Cancer).
- Gyara fatar jarirai da sanya su natsuwa da bacci.
- Hana rubewar hakori, kogon hakori da sauransu.
- Kariya daga ciwon asma da cututtukan numfashi.
- Rage hawan-jini.
- Rage yawan sinadarin “Cholesterol”.
- Kariya daga ciwon-suga.
- Inganta lafiyar kwalkwalwa da sauransu.
DOMIN SAMUN LAFIYAYYAR FATA;
Ana hada Man Zaitun da Man Ridi a mayar da shi abin shafawa a wata daya fatar jikin Mutum zatayi kyau kuma ta samu kariya daga Fungal Infection.
CIWON MARA;
Ana shan cokali 2 safe da rana da dare dan maganin ciwon mara.
CIWON CIKIN DA BAYAJIN MAGANI;
DA KURAJE MUSAMMAN NA KAZWA;
A samu sabulun Zaitun a riqa wanka da ita idan aka bushe sai a shafa Man ridi a kalla ayi haka sau 2 a Rana tsawon sati daya.
CIWON SIKILA;
Ana hada man Ridi da Zuma a riqa bawa mai matsalar yana shan cokali biyu safe da rana da dare har tsawon wata 2.
BASIR MAI TSIRO;
A samu Sassaken Bagaruwa da ‘ya’yan ta a tafasa da ruwa idan suka tafasa idan sun rage zafi sai a zauna cikin ruwan tsawon minti 15 idan aka fita a shafa Man ridi ayi haka sau 2 kowacce rana
tsawon kwana 10.
ASHMA;
A rika shan cokali 2 safe da rana tsawon sati 3.
ULCER;
A samu Man Ridi a hada da Madara a riqa sha da safe kafin aci komai haka da dare bayan anci komai sai asha awa daya kafin a kwanta.
KUMBURIN JIkI;
Ana shafa man ridi duk bayan anyi wanka da kuma in za’a kwanta bacci.
SOSHE SOSHE SABODA YAWAITAR MAJINA KO MATACCEN JIN:
Sai a saka cokali 2 duk lokacin da za’aci abinci sannan kuma a shafe jiki da shi amma wajen shafewa dole sai an hada da Man Zaitu.
CIWON MARA LOKACIN FARA AL’ADA:
Ana hada cokali daya na garin Ridi da cokali daya na man Ridi da madarar gari a sha sau 3 kullum In shaa Allahu za’a samu sauqi.
WANDA YAKE DA HAWAN JINI KO
MATCCEN JINI DA SAURANSU SAI YA
RINKA AMFANI DA MAN RIDI SAFE
DA YAMMA.