WANNAN MATSALAR TA DAUKEWAR NI’IMA GA MATA BAQARAMAR MATSALA BACE INSHALLAH XA’A SAMI WARAKA
FEMININE DRYNESS: (Bushewar gaba ko daukewar ni’ima) : Wannan na nufin karancin ni’ima ga mace kamar yadda matan sukafi fada. Amma masa kiwon lafiya kan ce karancin lubrication a farjin mace inda hakan ke jawo jin zafi Yayin saduwa, rashin dadin jima’i, rashin sha’awar yi da kuma kaikayi cikin farji.
Hakan na faruwane adalilin ko sakamakon karancin sinadarin hormone mai suna Estrogen a jikin mace, wanda ita take Samar da damshi cikin al’aurar mace dama sauran mahimman abubuwa a jikin mace da kara jin dadin gamsuwa.
Kamar yadda mukace karincin sinadaran hormone mai suna estrogen ke jawo bushewar farji, to me yake kawo karan sinadaran estrogen : gasu kamar haka :
Shayarwa
Magungunan Cancer.
Damuwa (Stress)
Tsaikon Al’ada
magungunan tazarar haihuwa.
matslar garkuwan jiki.
Ga wassu matsaloli da za suyi iya kawo matsalar Bushewar gaba:
Tsiron cikin mahaifa wato (fibroid).
Matsalar dakan shafi cikin mahaifa wadda ba Kari ba.
Tiyatar kwayayen haihuwa a mace (ovaries) watakil ko adalilin cyst.
Motsa jiki fiye da kima (Intense exercises).
Sai kuma amfani da sabulai, omo, mayuka, turare da mata suke amfani.
Matsalolin da Bushewar gaba zai iya kawowa mata
yakan iya bada daman shigar kwayoyin cuta
Jin zafi Yayin saduwa, musamman idan namijin bai iya foreplay ba.
Rashin gamsuwa.
kaikayin gaba
Jini lokocin saduwa.
Ya za’ayi a magance wannan matsalar:
Magani ya danganta da abinda binkice ya nuna, Duk mai fama da wannan matsalar ta daure taje ta sami kwararrun jami’an lafiya musamman wanda suka karanci bangaren mata (Gynaecologist) don su dubata su bata magani.