Yadda wata jarumar fina fina hausa ta bayyana cewa Ina Mamakin Yadda Mutane Suke Yi Wa Ƴan Fim Kallon Marasa Tarbiyya. Domin Ni Mahaifina Da Kansa Ya Kai Ni Masana’antar Kannywood, Inji Aisha Umar ” ta Cikin Shiri Mai Dogon ZangoA Duniya.
Jarumar ta bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai na gidan radio, freedom dake kano state yayin zantawa da ita cikin wata hira da ake gudanar da yan kannywood duk karshen mako, ta bayyana irin abubuwan da kallon da jama”a sukeyi musu na rashin fahimta a tattare dasu.

Aisha umar ta bayyana cewa yakamata al’umma suna fuskantar wasu abubuwa tattare dasu domin abinda mutum zai gudanar dashi a cikin fiim, to maganar gaskiya a zahiri ba haka mutum yake ba sabanin yadda wasu daga cikin al’umma suke musu kallon marasa tarbiyya.
Sana’ar fiim ta kasance daya daga cikin abubuwan da nafiso a cikin rayuwata kuma idan darai da lafiya watarana aure zanyi idan kuma nayi aure duk yadda nakeson gudanar da sana’ar fiim, to tabbas zan barta domin ganin na bawa mijina kulawa ta musamman cewar jarumar aisha umar ta cikin shiri mai dogon zango na aduniya series.