Da Bola Ahmed Tinubu Ya Mulke Mu Gara Muyi Tattaki Mu Koma Nijar Da Zama Har Sai Ya Sauka Daga Mulki Kafin Mu Dawo, Cewar Wasu Matasa Maza Da Matan Su ‘Yan Kwankwasiyya Daga Garin Ganjuwa A Jihar Bauchi.
Wasu fusattun matasa ‘yan hakidar tafiyar Dr. Rabi’u musa kwankwaso dan takarar shugaban kasar nigeria reshen jihar bauchi sun bayyana cewa basuji dadin rashin nasarar da sukayi ba a zaben da aka gudanar na wannan shekara 2023.
Matasan suka kara dacewa bola ahmed tinubu bai dace da mulkin nigeria ba hasalima lokacin da yayi gwamna a jihar Lagos mutanan arewa basuji dadin mulkin daya gudanar ba, a wannan lokaci kuma taya zai kamanta adalci.
Wannan dalili yasa zamuyi hijira izuwa makwabciyar kasar mu wato Niger, domin komawa chan da zama har zuwa lokacin da zai kammala mulkin nasa cewar matasan yan kungiyar ta kwankwasiyya dake jihar bauchi state nigeria.