Mene Ne Illar GB WhatsApp?
Mutane da dama ne ke amfani da wasu nau’ukan WhatsApp, da suka hada da WhatsApp Plus da GB WhatsApp da sauransu.
WhatsApp na cikin manyan kafofin sadarwa na tura sakwanni ta wayoyin salula da aka fi yawan amfani da su a duniya.
Ana amfani da su domin cutar mutane ta hanyar yi masu kutse. Idan ba mutum ya fita daga ire-irensu ba to yana cikin hatsari,
Mutane da yawa suna amfani da GBWhatsapp ne, saboda yana da wasu tsarurruka da ‘Whatsapp’ na asali ba shi da su, kamar irin su adana (sabing) na hoto, bidiyo, ko kuma kwafin rubutu daga ‘status(es)’ na mutane kai tsaye, ko boye alamar karantawa ko karbar sako, ko don yana nuna alamar in mutum yana online, ko don tura ‘file’ mai nauyi, ko boye groups/chats, ko rubuta sunan ‘group’ da harafai sama da 35, yin status da harufai 250, a takaice. GBWhatsapp yana da wasu ‘features’ da normal whatsapp ba shi da su.
Amma, yana da kyau mutum ya sani cewa duk wadannan tarko ne na masu kutse ko madatsa ‘hackers’. Sun tsara shi ne ta yadda zai ba ka sha’awa sosai, fiye da manhajar WhatsApp na asali (normal Whatsapp), tare da ba ka damar wasan buya da ma’abota amfani da normal Whatsapp, musamma ma mata. Ka tura sako, a karanta, amma ba za ka ga alamar an karanta ba, sannan a duba status dinka ba tare da ka ga wanda ya gani ba.
To dai maganar gaskiya, kai tsaye, GBWhatsapp, ‘mod’ ne, ma’ana ba asalin Whatsapp ba ne. Asali an kirkire shi da ‘code’ (tsari) irin an Whatsapp na gaskiya, ba tare da samun lasisi daga kamfanin ba. Ina shawartar masu amfani da GBWhatsapp, da masu sha’awar amfani da shi, da su kauracewa manhajar saboda wadannan dalilai; shi GBWhatsapp ba sahihi ba ne daga asalin kamfanin Whatsapp, ‘AledMods’ ne suka yi shi, ba su da lasisi, kuma sun karya ka’idar kirkirar da ba da lamunin amfani da sirrikan jama’a. Shi ya sa ba za ka samu manhajar a Google Playstore (apk) ko AppStore (iOS, na Apple) ba. Kai! Ka ma taba ganin wani adireshi na yanar gizo na GBWhatsapp? Amsa babu, saboda ba su da gaskiya.
Mai amfani da GBWhatsapp, ya sani cewa duk wasu bayanai da suke cikin wayarsa, wannan manhaja na iya tattarewa, babu wani sirrin cikin wayarka da ba za su iya lekawa ba, sayarwa, ko amfani da shi a duk lokacin da suka dama.
Idan aka turo ma wani sako mai dauke da ‘birus’ GBWhatsapp ba shi da wasu matakan kare ka daga cutarwarsu. Kai! Shi ma kansa ‘spyware’ ne. Duk abin da kake a GBWhatsapp, tsirara kake, shi ya sa, yawancin wadanda ake musu kutse (hacking) na Whatsapp, masu amfani da Whatsapp Mods ne, irin su GBWhatsapp, WhatsappPlus, Whatsapp Gold, Clones, FMWhatsapp, OGWhatsapp, YOWhatsapp da sauransu.
GBWhatsapp ba ya restore (dawo da bayanai) a wasu lokutan, kamar yadda na fada a sama, asali manhajar ta saba wa tsarin Google, kuma ana backup ne (yawanci) da Google account. Shi ya sa, da zarar ya yi ‘edpire’ (wani lokaci) za ka rasa duk bayananka, har ‘groups’ da kake ciki, sai ka nemi a maida ka. Ka lura, a duk lokacin da ka dauko shi daga yanar gizo, in dai wayarka tana ‘security patching’ (kula da tsaro), za ta gargadeka cewa, wannan app din zai iya cutar da kai, ko bayananka, ba ka taba lura ba ko? In ka taba lura da haka, don me za ka yarda?
Kai tsaye GBWhatsapp na mayaudara ne, in ba su cuceka yau ba, za su iya cutar da kai gobe. Kuma a kowane lokaci, Whatsapp na asali, za su iya dakatar da mai amfani da ‘mods’ daga amfani da dandalin na har abada.
Daga farkon watan nan dai zuwa yanzu, GB Whatsapp ya fara goge ‘formatting’ na wayoyin mutane. Sai ka bude wayarka, sai ka ga an goge komai dake cikinta. Idan kana amfani da shi, ka yi gaggawwar cire shi, tun kan hakan ta faru da kai.
Kuma ma inaso kasani a kowanne lokaci Whatsapp na asali za su iya dakatar da mai amfani da ‘mods’ daga amfani da dandalin.