Tips Na Girke Girke Daya Kamata UWARGIDA Ta Sani

Yakamata Koh wacce mace ta rubutasu ta aje sunada muhimmanci sosai

đŸ—¯Idan mai yayi yawa a abinci yaxaki yi ?
idan Mai yayi yawa musamman a jallop.sai ki jefa kankara zaki ga mai yataru guri daya akan kankara.

đŸ—¯idan abincin ki yakone yana warin kauri yaxa kiyi.?
idan abincin ki musamman shinkafa ya kone yana warin kauri ki sauke kisa 2slise bread akan abincin ki rufe yadan yi 3mints duk warin kaurin ze koma ga bread din.

đŸ—¯idan yaji yayi yawa ga abinci yaza kiyi?
idan yaji yama abinci yawa sai ki matsa lemun tsami aciki.

idan kika cika gishiri ga abinci yaza kiyi.?
idan gishiri yayi yawa sai ki jefa dankalin Hausa acikin miya ko abinci, dankalin nada zaki zaki janye gishirin.

KUSKUREN DASUKE BATA GIRKI

GISHIRI
idan kinsan girkinki ke kadai ce kobeda yawa kiguji yawan amfani da gishiri domin kuwa muddin kina saka wadataccen maggi to gishiri zedinga miki yawa

FRIDGE
duk abinda kikasan zaki barshi ya kwana kiguji saka mishi kwai ko kuma madara musamman idan ba fridge zakisa ba

KIFI
kilura gurin sarrafa kifi beson jagwalgwale hannu yana saurin bata kifi kidinga kulawa

KANWA
idan kanwarki bata da kyau kobaki da isasshiya kokuma baki da ita to karkiyi danwake domin kuwa bazae taba yin dandanoba hakanan kada kice zaki yawaita shi

SPAGHETTI
sphagetti batason spices dayawa hakanan bata son adafa ta da tafassahen nama ko ruwan nama dandanonta beyin dadi sedae kisoya nama kijefa aciki ko kuma kisaka mata kifi hakanan koda wasa karkisakawa sphagetti kitse

CHIPS
kilula idan zaki soya chips gishiri kawae ya wadatar karkice zaki saka maggi hakan ba gata bane taste din bekai na gishirin dadi

MASA
Idan xaki waina wato masa ki kula sosai albasa tana kara dadi amma idan tayiwa waina yawa tana bata taste din karkice zaki kwaba ta da albasa koki markada yana sakawa albasar tajima tana bugan kullin har taste din ya chanja.

DADDAWA
Ita daddawa tana qarawa abu armashi ba ayin farfesu babu daddawa ki kula koda na kifi ne daddawa itace sirrin farfesu hakanan cikawa farfesu Mai ko manja nasa taste din yakoma wani abu daban

BLACK TEA
kikula wajen dafa black tea bakowanne irin ganyayyaki ake sakawa ba anfison ganyen yazamanto kala guda sauran kuma kayan kamshine idan bahaka ba zeyi daci ko bauri

PEPPER MEAT
kikula gurin yin peper meat ko chicken dole sekin dan soya sannan kisake hadeshi idan bahaka ba zeyi karni

TAFARNUWA
Ita tafarnuwa anfiso asoyata ne afarkon girki nanne taste din yake dadi amma karkice zaki zubata akarshen girki zaki gagara ci musamman miyar kadi hakanan ba asaka tafarnuwa a alale ko dambu da makamantansu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *