Wata hira da ta gabata tsakanin wata tsohuwa yar shekara 50 da yar wata Jarida ta fito da sirrikan hakan:
Yar’jarida: Menene sirrun jin dadin zamantakewa tsakaninki da mijinki, Shin kin Kware ne wajen yi masa girki? Ko kuma Kyakyawace ke? ko dai kece uwar Iyalinsa?
Tsohuwa: Jin dadin zamantakewa tsakanin Ma’aurata dace ne daga Allah, amm mace na bada gudumawa wajen tabbatuwar haka, domin mace na iya maida gidan mijinta cikin walwala kamar yanda zata iya maidashi cikin kuncin rayuwa.
Ba wai sai da kudi ba domin da yawa daga cikin mata masu kudi suna cikin kuncin rayuwa.
Yawan ‘ya’ya ba shi ke kawo jin dadin rayuwa ba domin kuwa akwai macen da take da fiye da mazajen ‘ya’ya goma amma kullum cikin damuwa take kai ta iya yiwuwama mijin ya saketa a karshe.
Daddadan Abinci kuwa bashi gida da maigida ke bukata ba da farko, sabo zaka ga mace tun safe har dare ba abin da take sai girki ga iya girkin amma kullum kukanta mijin baya kyautata mata.
yar’jarida: To Menene Sirrin?
tsohuwa: Yayin da ran mijina ya baci shiru nake ina saurarenshi sauraro da ke cike da nutsuwa da nuna nadama akan abin da yake tuhumata dashi ina gyada kaina don nuna cewa ina sauraron bayanansa kuma na yarda dasu. Idan kika yi shirun kada ki kuskura ki rinka nuna masa cewa kece da gaskiya ko ya zalunceki a tuhumar da yake miki sabo da maza suna da mutukar tsikayen yanayi.
Yar’jarida: Me yasa bazaki fice ba idan ya fara fadan ki kyaleshi.
tsohuwa: Kar ki kuskura ki yi haka, sai ya ga kamar gudunshi kike ko maganganunshi basu dameki ba. Kawai ki yi shiru kina sauraran jawabansa kuma ki nuna yarda a duk abin da ya gaya miki har sai ya sauka daga fushinsa, sannan sai ki fita ki bashi wuri domin a lokacin jikinsa na bukatar ya dan huta kadan.
Yar’jarida: Daga nan kuma sai yaya? Zaki daina yi masa maganane tsawon kwanaki ko yaya?
tsohuwa: Kada ki gwada wannan halin domin kuwa sai ya saba da hakan a karshema ya fara cusguna miki ta hanyoyi daban daban.
Yar’jarida: To Me ya kamata ayi?
tsohuwa: Bayan kimanin awa biyu sai ki yi masa wani abin da zai dan sa abakinsa na sha ko na Taunawa, na tabbata ba zai ki karba ba, a take zaki ji ya fara miki magana cikin taushin murya yana nuna nadama kan yadda yazo ya fada ki da fada, Kai ta yiwu ma ya tambayeki: “Kin ji haushin fadan da na fadaki dashi?” sai kice : “aa” ai gaskiyace ka gayamin, kuma bazai sake faruwaba insha Allah.
Yar’jarida: Kuma kin yarda da hakurin da ya baki?
tsohuwa: E mana sabo da ai ni ba sokuwa bace, ta yaya zan gaskatashi yayin da yake cikin fushi kuma inki gaskatashi bayan ya dawo hayyacinsa.
yar’jarida: Mutuncin ki fa?
Tsohuwa: mutuncina shine neman yardar mijina da kyautata zamantakewarmu ni da shi, kuma wane mutunci mace ke dashi mutukar tana tsayuwa gaban mijinta ba tufafi a jikinta, shi kadai yasan sirrukanta da ba wani mahluki da ya sansu sai shi. To ina mutuncin da ya wuce miijinta?
Wani mai hikima yace:
Da tsuntsu Allah ya halicci mace da Dawisu zata zamo
Da kuma Dabbace da a bareyi zaa halicce ta
Da kuma kwaroce tabbas da cikin Mallam Fata-Fata zaka ganta.
To sai Allah yayita Mutum kuma aka halicceta da kashin hakarkari na hagu domin ta zam kusa da zuciya abar kauna a Matsayin Mata, Uwa, ‘Ya, Kanwa ko Yaya.
Allah yasa Mata su ji wannan Nasihar hakika zaa rage yawan sake-sake da suka yi kakagida a cikin al’ummarmu.
ya Allah ka zaunar da mu lafiya a gidan mazajenmu ka bamu ikon yi masu biyayya kamar yarda addini ya koyar. Aamin