Na ambaci tsarki ne don faɗaɗawa, amma da wankan janaba, dana haila, ko juma’at dana jinin biqi duk suffar iri daya ce kurum niyya ce ta bambanta.
TOH AMMA BARI MU ƊAU BAYANIN NA JANABA A AIKACE DON SHI AKA FI YI AKAI-AKAI
Tashin farko Bayan ka debi ruwanka a robar wanka ko bokiti mai tsarki da
tsarkakewa ka kai bandaki.
Sai kayi waɗannan abubuwa
Farawa da karkato bakin robar ko amfani da kofi ka debo ruwa ka wanke hannuwanka kafin fara wankan.
Saika ɗaura niyyar wankan (Nawaitul gusulul janabati) basai ka furta ba amma aranka zaka qudurce hakan.
Sai ka tsarkake Al’aura tare da istinja’i matsowa ahankali ka wanke abinda ya
makale na (Maniyyi) daga kororon mafitsara. Zaka wanke sau uku ko abinda ya sauwaka ka tabbatar de ya wanku
Sai yin Alwala irin yadda akeyinta inza ai Sallah wato har zuwa shafar kai… Toh saide bambancinta da alawar sallah shine a iya shafar kai zaka tsaya ba zaka wanke Kafafuwanka
ba tukun.
Daga nan bayan shafar kai saika sa yatsun ka duddurza gashinka kamar wanda za’ai ma aski da aska… Saika debo ruwa da hannunka ka wanke kan sau uku, tare da
tabbatarwa ruwan ya shiga ko ina, har ƙarƙashin gashin kai musamman a Mata saboda gashinsu nada tudu da yawa.
Saika tsaga jikinka biyu ka rika Zuba Ruwa kana cudawa a bangaren Jikinka na Dama tunda tsakiyar kanka har zuwa fuskarka, wuyanka, kafadarka, hannun dama, kirji, ciki, mara, cinyar kafa zuwa karshen yatsun kafar na dama…. Wato tsagin jikin. Dama kasan a alwala baka wanke kafafu ba toh anan ne inka gangaro zaka wanke kafafun
Bayan gamawa da bangaren dama saika kuma zubo ruwa daga tsakiyar kan har zuwa kafafunka da yatsun kafar.
Kaga daga nan ze zamto ko ina na jikinka ya sami ruwa shikenan ka idar da wankan janaba na SUFFATUL KAMALAH
TOH IDAN KUMA SWIMMING POOL NE KO KUWA SHOWER
Malamai sunce a irin wannan yanayin abinyi kurum shine: kai tsarki saika kudurci niyyar wankan da zakai saika auka cikin swimming pool ɗin shikenan, inka tabbatar ka jiqu ko ina na jikinka ya taɓi ruwa saika fito ka daura alwala kamar yadda akeyin ta sallah amma a wannan alawar ita har kafafu zaka wanke complete… Shikenan wankan janaba ya kammala.
Haka ma in shower ce, bayan kai tsarki saika kunna ka saki ruwan baki daya duk jikin… Inka gama saikai alwala shikenan. (Suffatul ijzah kenan)
KADA A MANTA ABUBUWAN DAKE HADDASA WANKAN JANABA SUNE
Idan anyi mafarkin saduwa da Mace ko
Namiji sai anyi wanka har ya zamto da aka farka anga maniyyi a tufafi toh koda ba a iya tuna mafarkin ba sai anyi wanka
Idan an sadu da Mace sai anyi wankan janaba Koda ta hanyar zina ne kuwa Allah ya kyauta.
Haka koda goge akaiwa Macen ajikin al’aurarta matukar maniyyi ya fita ko kuwa kan kaciyar namiji ya buya acikin farjin Mace toh koda ba’ai inzali ankawo maniyyi ba wanka ya kama mutum
Hakama masturbation na wajabta wankan janaba Allah ya sauwake.
Niyyar wanka a Zuciya ake kudurtawa ana iya yinta tun kafin ma ashiga bandakin basai anfurta ba. Wallahu a’alam.