Abubuwan bukata sun hada da
- Kwai guda4
- Sugar rabin Kofi
- Yeast cokali1
- Fulawa kofi2
- Flavor
- Mangyada rabin Kofi
Da farko za a zuba kwai a mazubi mai kyau a zuba sugar,yeast a kadasu sai a zuba fulawa a muka su hade jikinsu sosai…
Bayan sun hade jikinsu za a mulmula dough din a mike sai yanka gunduwa-gunduwa a mulmula kowane yanka kamar ball sai a rife shi for some 30mins sai a soya a ruwan mai yayi golden brown. Shikenan an kammala sai ci.
Za a iya cinsa as breakfast da tea ko zobo ko wani drinks hakan.ko kuma ayi domin motsa baki..