Doya
Kwai
Fulawa
Seasoning
Ki fere doyarki ki yanka Kamar yankatan kamar yankan nan ki zuba a tukunya ki saka suga da gishiri xaki iya saka curry kadan inkinaso tayi kala idan ta dahu bawai luguf sosai ba ki sauke ki tace ki rufe ki samu bowl dinki ki fasa kwai ki zuba ki kawo albasa da spring onion ki kada ki ajiye saiki dauko wata robar ki zuba fulawa ki saka Maggi ki dauko doyarki ki tsoma acikin kwai ki dawo da ita cikin fulawa ki saka ki juya ki maida ta cikin Kwan saiki saka a cikin Mai ki rage wuta haka xakita soyawa harki gama