Da farko ina neman addu’a ga duk Wanda ya karanta ya karu,Allah ya biya mana bukatumu na alhairi.
Sanyin kirji
A tamna saiwar zogale a tareda citta kwara daya.
Tsutsar ciki
A tafasa saiwar zogale da jar kanwa a sha.
Ciwon sanyi ga mata da maza
A tafasa saiwar zogale da kwara daya na tafarnuwa a sha sau biyu ga wuni tsawon kwana uku.
Yawan ruwan maniyi ga namiji
A gauraya cokali daya karami da sachet daya na madara.
Tarin sanyi ko Mura A gauraya garin saiwar zogale da zuma a sha cokali daya a kullum da safe tsawon sati daya.
Rage nauyi ko qiba
A tafasa saiwar zogale da lemun tsami daya a tace a sha bayan an karya sau daya a kullum
Zafin fitsari
A tafasa saiwar zogale da kanumfari a aha sau uku safe da rana da yamma.
Ciwon sugar
A zanka cin garin saiwar zogale a cikin abinci.
Qazuwa
A gauraya cokali daya na garin saiwar zogale da man zaitun a sha
Ciwon daji a cikin baki
A tafasa saiwar zogale a marmasa gishiri a kurkure baki dasu a kullum sau uku,safe da rana da yamma
Ciwon yatsa na Dankankare
A gauraya kwata na karamin cokali na garin saiwar zogale da na lalle a dorawa yatsan dake ciwo.
Matsanancin ciwon kai na zafi.
A yi hayakin saiwar zogale da garin habba.
Ni’ima ga mata
A tafasa saiwar zogale a tace ruwan misalin kwara daya na karamin cup sai a zuba rabin gwangwanin madara a sha.
Idan kun ji dadin wannan post din sai a yi shere wasu su karu.
A yi man addua ita ce goron sadaka.