SIRRIN GYARAN FATAR JIKIN AMARE

SIRRIN GYARAN FATAR JIKIN AMARE

amarya da take so jikinta ya dinga kyau da laushi fata to ta nemi wadannan.

man zaitun.
man za’afaran.
habbatus-sauda.

Sai a hada su a kwalba daya a girgiza, idan za'a kwanta barci sai a shafe jiki dukkansa, idan an tashi da safe sai ayi wanka a shafa man shafawa, indai Ana haka to fata zata yi kyau, kuma zata yi laushi sosai, kuma kuma zata yi haske na musamman.

SIRRIN GYARAN FATAR JIKIN AMARE

Idan mutum yana so fatarsa tayi kyau to idan gari ya waye kafin yaci komai ya sami ruwa Mai kyau Kofi daya ya sha.

ABIN DA YAKE JAWO WARIN JIKI

abin da yake kawo warin jikin shine:

wani halitta ce:

haka aka halicce shi,

wani kuma kazanta ce da rashin gyara.

Wai mutum ya kwana biyu bai yi wanka ba, sannan kwana a guri Mara kyau yana kawo warin jiki sannan yin kwaskwarima ita ma tana kawo warin jiki.

SIRRIN HANA WARIN JIKI

idan mutum yana fama da warin jiki to ya sami alimun(ALAM) ya dinga tsomawa a ruwan wanka safe da yamma, sannan ba sabulu ake yin wanka ya dinga yin amfani da hannusa yana dirzawa ko ina

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *